* Kuma za ta karrama Ayuba Ɗanzaki da amaryar sa
ƘUNGIYAR Marubuta ta Nijeriya (Association of Nigerian Authors, ANA), reshen Jihar Kano, ta ce za ta gudanar da wata muhimmiyar bita ta musamman don koya wa masu sha’awa yadda ake rubutun Hausa a bisa ƙ’a’ida, dokoki da kuma sharuɗɗan rubuta shi.
A sanarwar da Mataimakiyar Shugabar ƙungiyar kuma jagorar Kwamitin Tsarawa da Gudanar da Karatun Hausa, Hajiya Maimuna Sani Beli, ta bayar, an ce za a yi hakan ne a jibi Lahadi, 5 ga Satumba, 2021, a wajen taron karatun Hausa na wata-wata da ƙungiyar ke yi inda ake baje kolin fasahar adabi daga membobi kamar yadda ta saba yi a duk Lahadin farko na kowane wata.
A wannan karon, ƙungiyar ta ce ta zo da wani sabon salo ne na yin bitar.
Maimuna ta ce, “Wani masanin yadda ake rubutu da harshen Hausa wanda malami ne a Kwalejin Shari’a da Ilimin Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano kuma yanzu haka ya na karatun digirin sa na uku, wato PhD, a Sashen Koyar da Harsuna na Jami’ar Bayero ta Kano, wato Malam Yusuf Salisu Sani, ne wanda zai koyar da wannan sanin ƙwarewar yadda ake rubutun Hausa.
“Al’amarin da hatta Hausawa da yawa su ke ƙiƙi-ƙaƙa da shi.”

A cewar mataimakiyar shugabar, wannan bitar na daga cikin wani sabon shirin ANA Kano da aka ƙirƙiro don kawo cigaban ɗan’adam da haɓaka iyawar sa, wato ‘Human Development and Capacity Building’ (HD&CB) don amfanar da ‘yan wannan ƙungiya ta marubuta waɗanda su kan gabatar da rubuce-rubucen su cikin harsuna biyu, wato Hausa da kuma Ingilishi.
Bayan haka, ta ce ƙungiyar za ta yi karatu na musamman don taya murna da fatan alkhairi ga ɗaya daga cikin membobin ta, Ayuba Muhammad Ɗanzaki, da amaryar sa.
“Don haka ANA Kano na lale da marhabin da rubutattun waƙoƙi, ƙagaggu kuma gajerun labarai da ma wasannin kwaikwayo daga membobin ta don cimma wannan buri,” inji ta.
Haka kuma ta ce, “Sai dai kar a manta, jigon wannan karatun karramawa zai ta’allaƙa ne a kan aure, kyautata shi da kuma ɗorewar sa.”
Za a gudanar da waɗannan lamura guda biyu ɗaya bayan ɗaya ne kamar haka:
1. BITA – Ƙa’idojin Rubuta Hausa 10:30ns – 12:00nr
2. KARATU – Karrama Ma’aurata 12:00nr – 2:00nr
An buƙaci mahalarta da su je taron da waƙa ko karatu da su ka shafi aure.

Za a fara taron da ƙarfe 10:00 na safe a Laburaren Murtala Muhammed da ke Titin Ahmadu Bello, Kano.
A cewar Maimuna Beli, fitacce kuma gogaggen ɗan jaridar nan sannan malami a Jami’ar Bayero, Kano, Dakta Isa Muhammad Inuwa, shi ne zai jagorancin taron.