A SAKAMAKON rashin da aka yi na babban malamin nan da ke Kano, Sheikh (Dakta) Yusuf Ali, Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Arewacin Nijeriya, wato ‘Northern Nigerian Writers Summit’ (NNWS) ta nuna alhini tare da jimamin ta na rasuwar.
A wata sanarwa da babban sakataren ƙungiyar, Malam Khalid Imam, ya bayar a ranar 12 ga Nuwamba, 2023, ƙungiyar ta ce: “Cikin jimami da girmamawa, Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Arewacin Nijeriya, mai suna ‘Northern Nigeria Writers’ Summit (NNWS) ta na taya al’umma alhinin rashin Dakta Yusuf Ali.
“Marigayin, wanda ya koma ga mahaliccin sa a ranar 6 ga Nuwamba, 2023 a garin Kano da ke arewa-maso-yammacin Nijeriya, ya rasu ya bar ‘ya’ya 27.
“Dakta Yusuf Ali, wanda tsohon alƙali ne kuma malamin addinin Musulunci, ya karantar da al’umma masu yawa. Bayan kasancewar sa shehi, muƙaddami a ɗariƙar Tijjaniya kuma mai sarauta, Yusuf Ali ya kasance marubuci ne na a nuna wa sarki.
“Marigayin wanda shi ne shugaban Malaman Masarautar Gaya, ɗaya daga cikin daɗaɗɗun masarutun ƙasar Hausa, ya rasu ya na da shekara 73.
“Rayuwar sa ta kasance ta gwagwarmaya tsakanin neman ilimi da bayar da shi.
“Wanda duk ya san shi to ya san shi ne a matsayin tinjimin malami kuma bajimin marubuci. Wannan ne ya sanya malamin, wanda aka haife shi a garin Gaya a shekarar 1950, ya yi ƙaura zuwa Kano a 1970 inda ya yi fice a cibiyar ta kasuwanci tun wajajen shekarun 1980.
“Irin wannan himma tasa ce ta sanya ya shigar da kan sa a makarantar zamani bayan ya yi karatun Alƙur’ani da littattafan ilimi a gida da waje wajen malaman sa.
“Yayin da ya shiga neman ilimin zamani, Sheikh Yusuf Ali ya yi tsayuwar daka har sai da ya kai ga ƙarshen alƙalami a fannin ilimin Musulunci inda har ya sami digirin digirgir daga Jami’ar Bayero ta Kano.
“Haka kuma ya yi aiki a ɓangaren Shari’a har sai da ya kai ga taka matsayin ƙoli a alƙalanci a jihar sa ta Kano inda ya ajiye aiki a shekarar 2009.
“Malam Yusuf Ali ya bayar da gudunmawa matuƙa wajen ilimintarwa da faɗakar da al’umma, musamman ta shirye-shiryen sa a kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen ƙasar nan.
Shahararren shirin sa na fatawa mai taken ‘Ilimi Kogi’ ya cancanci a ambace shi.
“Malamin, wanda marubuci ne musamman na waƙoƙin Hausa kuma makaranci ne na duk littattafan adabi da sauran ilimai, ya cancanci dukkan marubuta da masu zumunci da adabi su yi alhinin rashin sa.
“Ɗaya daga abin da ya ke nuni da himmar sa a fagen ilimi da son karatu shi ne labarin da ɗiyar sa wacce malama ce a jami’a ta bayar a shafin ta na Facebook cewa har ya na gadon asibiti Shehin bai gushe ba ya na neman a ba shi littafi ya karanta.
“Tabbas, marubuta sun yi rashin ɗan’uwan su, kuma jigo a harkar rubutu da adabi; wanda tarihin adabi ba zai manta da shi ba. Rubuce-rubucen sa za su sanya a ci gaba da tunawa da shi har bayan bayan sa, kuma zai kasance ya na rayuwa bayan wafatin sa.
“Don haka NNWS ta na taya iyalan sa da almajiran sa da dukkan jama’ar Nijeriya alhinin rashin sa.
“Da fatan Allah ya jiƙan sa, ya ba da haƙurin rashin sa.”