ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Jihar Katsina, wato ‘Katsina Film Makers Association’, ta kai wata ziyara ta musamman ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a jiya Laraba.
Membobin ƙungiyar sun samu kyakkyawar tarba daga Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, tare da daraktocin sa.
Maziyartan, a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Alhaji Aminu Mannir K-eza, sun haɗa da mataimakin sa, Lawal Ibrahim Bawan Mata, da sakataren ƙungiyar, Malam Aminu Abdullahi, da wasu daga cikin shuwagabannin ƙungiyar.

An yi zama na musamman inda aka tattauna muhimman batutuwa, ciki har da gabatar da ita kan ta ƙungiyar tare da taya shugaban hukumar murnar samun matsayi da ya yi.
A jawabin tarbar su da yi, El-Mustapha ya bayyana matuƙar nuna jin daɗin ziyarar.
Ya ce, “Ana tare shekaru da yawa baya, to ga dama ta samu wacce za a ƙara cicciɓa harkar kuma a tsaftace ta, kamar yadda da ma Katsina da Kano Ɗanjuma ne da Ɗanjummai.”
Sannan ya bayar da shawarwari, waɗanda ya ce idan aka bi su za su ƙara kawo cigaba a cikin masana’antar Kannywood da kuma haɗin kan da zai ƙara sa a zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, musamman Katsina da Kano.
Bayan ya yi godiya game da ziyarar sai aka rufe taro da addu’a.