ƘUNGIYAR Tarayyar Afrika (AU) ta zaɓi Swahili, wani harshe da aka fi yin amfani da shi a yankin Gabashin Afrika, a matsayin yaren da za ta riƙa amfani da shi a hukumance cikin al’amuran ta na yau da kullum.
Kafin wannan lokaci, ƙungiyar ta na amfani da Larabci, Ingilishi, Faransanci, yaren Focugal da Sifaniyanci ne a al’amurran ta.
A yanzu kuwa, Sashe na 11 na Dokar Garambawul kan Tsarin Mulkin Ƙungiyar Tarayyar Afrika ya ce: “Harsunan da za a riƙa amfani da su a hukumance a Tarayyar da dukkan cibiyoyin ta za su kasance ne Larabci, Ingilishi, Faransanci, yaren Focugal, Sifaniyanci, Kiswahili da duk wani yaren na Afrika.”
An yanke shawarar amincewa da Swahili ne, wanda kuma ake kira Kiswahili, a babban taron kwana biyu na shugabannin ƙasashen Afrika da aka yi a hedikwatar ƙungiyar da ke birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, bayan buƙatar hakan da Mataimakin Shugaban ƙasar Tanzaniya, Dakta Phillip Mpango, ya kai a gaban taron.
A bayanin da ya gabatar na wannan buƙata, Dakta Mpango ya ce Swahili ya na daga cikin harsunan da aka fi yin amfani da su a Afrika, ya ce akwai masu amfani da shi kimanin miliyan 100 a ciki da kuma wajen nahiyar.
Ya ce: “Har ma an fara amfani da Kiswahili a ƙungiyoyi da dama waɗanda su ka haɗa da Ƙungiyar Ƙasashen Gabashin Afrika (EAC) da Ƙungiyar Cigaban Ƙasashen Kudancin Afrika (SADC), sannan kuma ana amfani da shi wajen koyarwa a makarantu a ƙasashen Afrika da dama.”
Bugu da ƙari, ya yi nuni da cewa Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ware ranar 7 ga Yuli ta kowace shekara a matsayin Ranar Yaren Kiswahili ta Duniya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a ranar Talata ne, 23 ga Nuwamba, 2021 a wajen taro na 41 na membobin ƙungiyar wanda aka yi a birnin Paris na ƙasar Faransa, UNESCO ta bada sanarwar an samar da Ranar Yaren Kiswahili ta Duniya, kuma za ta fara aiki daga ranar 7 ga Yuli, 2022.
Mujallar Fim ta ce hakan ya sa wannan yare ya zama yaren Afrika na farko da UNESCO ta amince da shi.
A saƙon da ta tura a Tuwita a ranar Talata, ƙungiyar ta ce, “Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware rana ta musamman domin karrama Kiswahili. Za a riƙa murnar zagayowar ranar da yaren a ranar 7 ga Yuli a kowace shekara. Dukkan membobin UNESCO sun yi na’am da wannan shawara, babu wanda bai lamunta ba.”
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, yaren Swahili ya samo asali ne a Afrika ta Gabas, kuma akwai masu amfani da shi a sama da ƙasashe 14, wato Tanzaniya, Kenya, Uganda, Ruwanda, Burundi, Jamhuriyar Dimokiraɗiyya ta Kwango (DRC), Sudan ta Kudu, Somaliya, Mozambiƙ, Malawi, Zambiya, Komoros, da ma ƙasashen Larabawa na Oman da Yemen da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Ƙasashen Kudancin Afrika irin su Afrika ta Kudu da Botswana sun fara amfani da harshen wajen koyarwa a makarantu, a yayin da Namibiya da wasu ƙasashen su ma sun fara tunanin yin hakan.