ƁARAYI masu garkuwa da mutane sun sace ɗaya daga cikin shugabannin harkar fim a Jihar Zamfara, Alhaji Ali Bulala Gusau.
An sace Ali ne tare da matar sa a kan hanyar Gusau zuwa Sakkwato a jiya.
Sai dai kuma a yau mujallar Fim ta samu labarin cewa ɓatagarin sun saki matar, amma kuma sun riƙe Alin tare da faɗa wa masu tattaunawa da su cewa sai an biya naira miliyan 30 kafin su sako shi.
Wata majiya ta ce a lokacin da ‘yan bindigar ke ƙoƙarin yin satar, sun yi musayar wuta da wasu jami’an tsaro, wanda ta hakan ne Allah ya kuɓutar da ‘ya’yan Alin daga hannun ɓarayin.
Sace babban furodusan ya girgiza masana’antar fim, musamman manyan masu shirya finafinan.
Da yawa sun yi addu’ar Allah ya kuɓutar da shi da iyalin nasa da gaggawa.
Wani shugaba a MOPPAN ya shaida wa wakilin mu cewa mai yiwuwa ne Aliyu da iyalin sa su na kan hanyar zuwa Jamhuriyar Nijar ne domin yi wa surukan sa gaisuwar Sallah.

Mujallar Fim ta sha buga labarin Aliyu a shekarun baya, ciki har da hirarraki da shi da kuma labarin auren da ya wo daga Nijar.
Ali Bulala Gusau ya na daga cikin manyan furodusoshin Zamfara.
Shi ne mashiryin fitaccen fim ɗin nan mai suna ‘Ki Yafe Ni’ wanda aka yi kimanin shekaru 15 da su ka gabata.
Lokacin da aka kafa Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa, shi ne aka zaɓa a matsayin Sakataren Kuɗi, muƙamin da kuma ya riƙe a MOPPAN.
Haka kuma ya taɓa zama shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Zamfara.
Mu ma mu na addu’ar Allah ya kuɓutar da shi, amin.
