• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɓatanci kan Kannywood: Lauyoyin Amdaz sun yi wa na Alhaji Sheshe martani

by DAGA ALI KANO DA MUKHTAR YAKUBU
November 17, 2023
in Labarai
0
Amdaz (a hagu) da Alhaji Sheshe

Amdaz (a hagu) da Alhaji Sheshe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

LAUYOYIN jarumi kuma mawaƙi a Kannywood,
Abdullahi Ɗan’azumi (Amdaz) a yau sun aika da martani a rubuce ga lauyoyin furodusa Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe), wanda a jiya Alhamis ya yi barazanar zai maka jarumin a kotu kan kalaman da ya yi dangane da ayyukan assha da ya yi iƙirarin ana aikatawa a masana’antar.

Idan kun tuna, jarumin ya furta kakkausan zargin ne a jawabin da ya gabatar a wurin taron da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi da ‘yan fim a ranar Litinin da ta gabata.

Kalaman nasa sun dugunzuma wasu daga cikin ‘yan fim, yayin da wasu kuwa su ke mara masa baya.

Alhaji Sheshe ya na ɗaya daga cikin ‘yan fim da jawabin ya yi wa ciwo, wanda ya sa a jiya Alhamis ya sanya lauyoyin sa su ka rubuta wa Amdaz takardar barazanar cewa ko dai ya janye kalaman sa ko kuma su maka shi a kotu.

To a yau a soshiyal midiya sai Amdaz ya wallafa shafin takardar da lauyoyin sa su ka aika wa da na Alhaji Sheshe.

A takardar falle ɗaya wadda mujallar Fim ta gani, lauyoyin, masu kamfanin ‘Humanity Associates’ da ke da adireshi a Sharaɗa, Kano, sun ce sun sadu da takardar da aka rubuta wa wanda su ke wakilta, wato Amdaz, kuma shi ne ya ba su umurnin su maida amsa.

Mujallar Fim ta fassara takardar tasu kamar haka: “Duk da yake mu na so mu ba ku amsa cikakkiya kan wasiƙar ku, amma mu na so ku fara da ba mu bayanai kan wasu abubuwa da mu ka lura da su a nan domin kada mu je mu na ɓata lokacin mu wajen musayar magana da wasu da ke yaudara da cewar su lauyoyi ne.

“Na farko, bincike a gurguje a gidan yanar hukumar CAC bai nuna akwai wani kamfani ko wani bayani da aka shigar ba kan ‘N & N Attorneys ‘, wanda hakan ya haifar da damuwa kan idan da gaske akwai wani kamfani da aka yi wa rajista da wannan sunan wanda mu ke magana da shi.

“Na biyu, an yi amfani da hatimin da ya daina aiki na wani mai suna Uba Nazeer Abdullahi, a yayin da ita wasiƙar ke ɗauke da sa-hannun wani mai suna Cif Nnamdi Onana tare da wasu.

“Na uku, a kan batun da ake magana, mu na ba ku shawarar ku samu cikakken kwafen jawabin na sauti, a rubuta shi a rubuce kuma a samu ƙwararriyar fassarar shi daga sauti, wato wanda ku ka ɗora zargin ku a kai, sannan ku faɗi daidai ainihin wurin da aka ambaci sunan wanda ku ke wakilta kafin ku yi iƙirarin cewa wanda mu ke wakilta ya yi ‘maganganu babu tunani, masu ɗauke da ɓatanci da kuma tozarci’ ga wanda ku ke wakilta.

Takardar da lauyoyin Amdaz su ka tura ga na Alhaji Sheshe

“Mun yi amanna da cewa babu wani lauya da ya amsa sunan sa wanda zai ɗauki kalaman wanda mu ke wakilta a matsayin ɓatanci ga kowane mutum sai idan shi mutumin…”

A daidai nan shafin wasiƙar da Amdaz ya wallafa ta ƙare, mujallar Fim ba ta samu kwafen shafi na biyu ba don ganin cigaban bayanan lauyan nasa.

Tun daga lokacin da wannan ƙurar da ta tashi, Amdaz ya fito a jiya ya bayyana cewa ya na fuskantar barazana ga rayuwar sa. Ya ce: “Ana yi wa rayuwa ta barazana saboda na faɗi gaskiya a kan abin da ya ke faruwa a Kannywood.”

Amma bai yi bayani a kan haka ba. Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a jiya ɗin, ya ce ba zai taɓa bada haƙuri ba kamar yadda lauyoyin Alhaji Sheshe su ka buƙace shi da ya yi.

Ya ce: “Na karɓi sammacin kotu, amma har Mahdy ya bayyana a busa ƙaho ba zan ƙaryata kai na ba. Kuma zan bi wannan takarda da Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, amma dai daga yanzu har Mahdi ya bayyana a busa ƙaho ban ga kotu ko wani ɗan’adam da ya isa ya saka ni ƙaryata kai na ba.”

Amdaz ya ƙara da cewa, “Ba sa’o’i 48 ba, har zaren agogo ya tsinke babu wanda ya isa ya sa ni ba da haƙuri a cikin haƙƙin Ubangiji, don haka duk abin da na faɗa na faɗa, ba zan ƙaryata kai na ba a kan wannan maganar.

“Tunda kun kasa kawo hujja ko ƙaryata abin da na faɗa, kawai ku karɓi gaskiya ku huta, ku yi umarni da kyakykyawa ku yi hani da mummuna.”

Jama’a dai a yanzu sun zuba ido su ga yadda wannan turka-turkar za ta kaya.

Loading

Previous Post

Kiran Tinubu ga editoci: Ku riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Next Post

Cika shekaru 57: Inda na fito da inda na sa gaba – Iyan-Tama

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama

Cika shekaru 57: Inda na fito da inda na sa gaba - Iyan-Tama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!