• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɗaliban jami’a ‘yan Nijeriya sun karrama Rahama Sadau a Indiya

by DAGA IRO MAMMAN
September 24, 2021
in Labarai
0
Rahama Sadau da wasu malamai a babban teburin taron karramawar

Rahama Sadau da wasu malamai a babban teburin taron karramawar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊALIBAI ‘yan Nijeriya da ke karatu a wata jami’a a ƙasar Indiya sun karrama fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, wadda a yanzu ta ke ƙasar domin ɗaukar wani fim.

Rahama ta je Indiya ne bisa gayyata domin fitowa a fim ɗin gumurzu mai suna ‘Khuda Haafiz’ kashi na 2.

Ana shirya fim ɗin ne a Lucknow, babban birnin jihar Utter Pradesh.

Ɗalibai da malaman Jami’ar Integral a wajen karramawar a Lucknow

Jami’ar, mai suna Integral University, makaranta ce mai zaman kan ta wadda ke cikin garin na Lucknow, kuma akwai ‘yan Nijeriya da ke karatu a cikin ta.

Ana gabatar da jawabai a wajen taron

Jin cewa ga Rahama Sadau a garin ya sa su ka kira ta domin su karrama ta saboda Hausawa sun ce kowa ya ga na gida, ya rasa ahu.

An ɗan yi jawabai da musabiha, inda aka gwarzanta jarumar tare da lissafa nasarorin da ta samu a fagen shirya finafinai a Nijeriya.

Wani malami ya na ba Rahama Sadau kyautar fulawar karramawa

A saƙon godiya da ta wallafa a Instagram a yau, jarumar ta bayyana jin daɗin ta, ta na faɗin, “Na yi matuƙar alfahari tare da jin daɗi da na samu gayyata daga ɗalibai ‘yan Nijeriya da ke karatu a ‘Integral University’ ta Indiya. 

“Na kasa ɓoye farin ciki na dangane da wannan kyakkyawar karramawa, wadda ke da muhimmanci sosai a gare ni.

Rahama tare da malamai da ɗaliban ‘Integral University’

“Ku ma ma’aikatan ‘Integral University’, kyakkyawar karɓar da ku ka yi mani abar so ce kuma abar godiya har abada. Sannan su ma ɗalibai masu sadaukarwa da ƙwazo na wannan jami’a mai mutunci waɗanda su ka shirya wannan taro domin karrama zuwa na, kun samu gurbi na musamman a cikin zuciya ta. Na gode da kyautar da ku ka ba ni da komai da komai. Soyayya mai yawa a gare ku.”

Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba ku labarin zuwan Rahama Indiya domin shirya fim ɗin na ‘Khuda Haafiz’ kashi na 2.

A nan ma jarumar ce tare da waɗanda su ka karrama ta

Kamfanin ‘Panorama Studios’ na masana’antar shirya finafinan Indiya, wato Bollywood, shi ne ya ɗauki nauyin shirya shi, kuma darakta Faruk Kabir ne ke bada umarni.

Kashi na farko na fim ɗin ya fito ne a cikin Agusta, 2020.

Ana yi wa Rahama Sadau rakiya lokacin da za ta koma masauki bayan an gama taron karrama ta

Sai dai har yanzu ba mu san rol ɗin da aka ba Rahama Sadau a cigaban labarin fim ɗin da ake ɗauka ba.

Loading

Tags: BollywoodFaruk KabirIndian filmIntegral University LucknowKannywoodkarramawaKhuda Haafiz Chapter 2 movieRahama Sadau
Previous Post

WAMMA Awards 2021 ta ba mu ƙwarin gwiwa, inji TY Shaban

Next Post

Haramcin fim kan kidinafin da daba: Ba zan iya faɗa da gwamnati ba – Asase

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Tijjani Asase

Haramcin fim kan kidinafin da daba: Ba zan iya faɗa da gwamnati ba - Asase

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!