• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɗanfodiyo: Ƙabilanci ko Jihadi?

by FATUHU MUSTAPHA
December 10, 2019
in Addini
0
Ɗanfodiyo: Ƙabilanci ko Jihadi?

Masallacin Shehu a Sakkwato

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A KWANAKIN nan na lura wasu ‘yan’uwa sun samu wasu bayanai na Turawan Yamma kan batun Jihadin Shehu Usmanu bin Fodiyo, wanda mafi akasari Turawan ne suka wallafa, inda kamar yadda suka saba, suka nuna cewa jihadin ba an yi shi ne don Allah ba, an yi shi ne don kawai tsantsar ƙabilanci.

Farkon wanda ya fara wannan magana shi ne Lord Frederick Lugard a jawabin da ya yi wa sarakunan Arewa, inda ya ce masu: “Fulani sun yi amfani da ɗaukaka ta ilimi da ƙarfin mulki sun ƙwace sarauta daga hannun Hausawa. Mu kuma yau mun ƙwace ƙarfin mulki daga hannun ku.”

Tunanin Lugard shi ne Fulani sun ƙwace mulki daga hannun Hausawa ne ba wai don addini ba, sai dai don sun fi Hausawa ilimi da kuma wayewa.

Wannan tunani, a kan sa masana na Orientalism irin su Hisket, Arnot, Wallace, Berth, Mischlich, Palmer da sauran su suka rayu. Sun yi ƙoƙari matuƙa wurin ganin sun daƙile kaifin tasirin Jihadin Shehu a ƙasar Hausa, amma abin ya ci tura. Wannan rashin nasara ne ya sanya Hisket a ƙarshen rayuwar sa ya nuna takaicin sa a littafin sa na ƙarshe da ya rubuta, a kan ƙarfin tasirin addinin Islama a zuciyar Bahaushe a littafin sa mai suna Some to Mecca They Turn to Pray.

Tunanin masana na Turai, tun a ƙarni na 16, shi ne an tursasa mutanen Sudan ta Tsakiya ne sun karɓi Musulunci, kuma ana ganin in an zo musu da mafita, za su iya barin addinin Islama su karɓi addinin Kiristanci.

Wannan gurgun tunani ne ya sanya a shekarun 1500s su ka shirya wata tawaga da su ka kira Borno Mission, da nufin yaɗa addinin Kiristanci a Borno. Wannan makauniyar hujja da manyan jami’an Kiristanci suka samu, ita ta sa suka turo wannan tawaga, wadda a ƙarshe dai ta ƙare a birnin Katsina, kamar yadda Lavers ya bayyana a ƙasidar sa wadda aka buga a kundin nan na History and State of Learning in Katsina.

Wannan bayani zai yi magana ne a kan shin Jihadin Ɗanfodiyo na ƙabilanci ne ko kuwa na addini? Shin wace rawa Hausawa suka taka a wannan jihadi? Shin jihadin ya cika sharuɗɗa na jihadin Musulunci ko kuwa?

Ba dai zan ɗau lokaci a kan batun addini da Jihadin Shehu ba, tunda ni ba malami ba ne; wannan ya na buƙatar masana su yi bayani, ba almajiri iri na ba. Sai dai in an duba, za a ga cewa sharuɗɗan yin jihadi sun tabbata in aka yi la’akari da dokokin da Sarkin Gobir na Wurno, Nafata, ya kafa wa Musulmi, na hani ga maza da mata da su yi duk wata shiga ta Musulunci, sannan kuma ya ma kafa dokar hana duk wani Bagobiri wanda ba Musulmi ba da ya shiga Musulunci, duk kuwa da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Shehu Usmanu da mahaifinsa Bawa Jangwarzo a ranar Sallah, kafin rasuwar Bawa.

Ina ganin ɗaya daga cikin sharuɗɗan yin jihadi: in har aka hana ku yin addinin ku a ƙasa, ko aka taɓa dukiyoyin ku. Waɗannan ukun kuwa duk sun faru a ƙasar Gobir a kan Shehu da mabiyan sa. In har wannan ya tabbata a Musulunci, musamman in aka yi la’akari da dokar da Nafata ya kafa, kuma magajin sa Sarkin Gobir Yunfa ya tabbatar, to lallai kuwa ya wajaba a kan Shehu da mabiyan sa su tashi tsaye domin kare addinin su da aƙidun su.

Wani abin da zai iya tabbatar da wajabcin Jihadin Shehu shi ne abin da a turance ake kira da syncretism, wato haɗe addini biyu a lokaci ɗaya, rabi Musulunci, rabi kafirci, wanda duk wani malamin tarihi ya tabbatar da wannan ruwan dare ne a ƙasar Hausa a wancan lokaci.

Tun kafin Shehu da kusan shekaru da dama, marubucin waƙar nan mai suna: “Shurb al Zulal” ya bayyana wannan ɗabi’a a cikin muggan ɗabi’u da suka yi wa ƙasar Hausa katutu, baya ga matsalar kore mutane daga Musulunci.

A cikin Tarikh Arbab mun ji yadda Sarkin Kano Kanajeji ya karɓi addinin maguzanci ya raya barayar Tsumburbura domin samun biyan buƙatar sa ta ya ci ƙasar Zazzau da yaƙi. A dai cikin kundin, mun ji yadda Sarkin Kano Alwali ya sha daga da al’adar nan ta Dirki, wadda ta jawo masa tsangwama a Kano.

Mun kuma ji irin dagar da Sarkin Katsina Gozo ya sha da manyan sarakunan Katsina, wanda har ta kai ga rasa ran sa a hannun manyan bayin Katsina, ƙarƙashin jagorancin Ƙauran Katsina Kuren Gumari, kamar yadda ya zo a kundin tarihin Katsina: Tarikh Umara’ Kashina wa Gubir.

Wani babban dalilin da addini ya wajabta jihadi shi ne yawaitar zalunci, musamman a fadojin sarakuna. Wannan kuwa ya tabbata in mu ka yi la’akari da hikayar Ƙunar Baƙin Wake da ta faru a Katsina, saboda zalunci da ya yi yawa.

Akwai irin waɗannan misalai da dama waɗanda ba za a iya kawo su a wannan wuri ba.

To, in har mun kalli abin a taƙaice ta fuskar addini, bari mu kalli abin ta fuskar ƙabilanci. Shin a iya kiran Jihadin Shehu a matsayin Jihadin Fulani? Maganar gaskiya in aka yi haka ba a yi wa Shehu da mabiyan sa da dama adalci ba.

Hujja ta Farko: Ummulhaba’isin rabuwar ɗaukar makami a fita jihadi, a kan wani malami ne Bahaushe, Malam Abdussalami. Domin shi fadawan Sarkin Gobir Yunfa suka kama, suka wulaƙanta shi, da shi da almajiran sa. Hakan ta sanya Shehu da almajiran sa suka fita suka ɗau makamai suka ƙwace shi, kamar yadda Murray Last ya kawo a littafin sa, The Sokoto Caliphate. Wannan malami shi ne wanda rigima ta ɓarke tsakanin sa da Sarkin Musulmi Bello, har ya rubuta littafin sa Sardar Kalam, fi ma jara, baini wa baina Abdussalam.

Hujja ta Biyu: Manyan malaman da Shehu ya ke jinjina wa a rayuwar sa Hausawa ne, wanda shi da Shehu da Abdullahi suka yi karatu a gaban su: Sheikh Hashim Bazamfari, wanda Shehu Abdullahi ya yi bayanin sa a littafin sa Ida ‘un nusk da kuma Shehu Jibrin Ghaini wanda Shehu Ɗanfodiyo da kan sa ya ke cewa a wata waƙar sa: “In An Tambaye Ka, Waye Ni?” Ka ce ni taguwa ce daga Taguwoyin Jibrilu” saboda tsabar biyayyar da yake masa. Shi wannan malami shi ne ya kai Ɗanfodiyo birnin Agadas. Duk da saɓanin ra’ayi da aka samu tsakanin Shehu da malamin nasa, bayan dawowar malamin nasa daga hijaz, saboda ya dawo da aƙidar Zahiriya, kuma har ma ya rubuta littafin sa Shifa al Ghalil, amma har ya rasu Shehu ya na jinjina masa.

Hujja ta Uku: Ya kamata mu sani, ba fa Fulani suka haɗu suka yaƙi Hausawa ba, akwai Hausawa da suka bi Shehu, musamman malamai, kamar yadda na kawo muku Malam Abdussalami, akwai irin su Shitu ɗan Abdurra’uf, wanda ya rubuta shahararriyar waƙar nan, Jiddul Ajizi, wadda aka fi sani da “Nagozo” (ya kira ta da wannan suna saboda a tuna da Sarkin Katsina Muhammadu Gozo), da kuma irin su Malam Muhammadu na Birnin Gwari (ana zaton shi ya rubuta “Bakandamiya”, wato “Gangar Wa’azu”).

A Barebari kuma akwai irin su Malam Yamusa, wanda sarakunan Haɓe suka kai shi zaman fursuna a Ƙaraye, daga baya Fulani suka ƙwato shi, ya zama Sarkin Zazzau na biyu.

Wani babban malamin kuma Bahaushe da ya taka rawa a Jihadin Shehu shi ne Alƙalin Kano, Usmanul Hausawi. Har ma yana cikin mutane uku da Sarkin Kano Sulaimanu ya aika Sakkwato a matsayin waɗanda yake fatan su gaje shi. Akwai kuma Malam Muhammadu na Alhaji, wanda ya na cikin mutum uku da aka bai wa tuta, kuma ya na cikin mutane uku da su ka fara sarautar Katsina: Umaru Dallaje, Umaru Dumyawo, da Muhammadu na Alhaji, duk a lokaci ɗaya suka zama sarakunan Katsina.

Hujja ta Huɗu: Ba Fulani kawai aka bai wa tuta ba, an bai wa har waɗanda ba Fulani ba. Na kawo Malam Muhammadu na Alhaji, to akwai sarakunan Haɓe da ma ko yaƙar su ba a yi ba saboda sun ƙulla aminci da Fulani. Misali, Sarkin Zazzau Jatau, sai bayan rasuwar sa Sarkin Zazzau Makau ya tada alƙawari, wanda ya sanya Fulani su ka yaƙe shi. Domin da saboda mulki suke, ai da ba za su bari ɗan sa ya gaje shi ba. Wannan tawaye da ya yi shi ya jawo jihadi a ƙasar Zazzau. Kuma ko da da Fulani su ka ci ƙasar Zazzau, ba su taɓar da gidan sarautar Haɓe ba, sun yanka musu masarauta a Habuja da kuma Jiwa. Kuma har yau su ke sarauta a waɗannan masarautu.

Hujjar ta Biyar: An bai wa Hausawa tuta, domin an baiwa Malam Yakubu tuta a ƙasar Bauchi. Kuma har yau jinin sa ke sarauta a ƙasar.

Da wannan na ke tabbatar da cewa Jihadin Shehu ba ƙabilanci ba ne. Jihadi ne na fisabilillahi.

Allahu a’alamu.

Loading

Previous Post

Shekara 5: Abin da ya sa har yanzu ba kamar Ibro

Next Post

Rahama Sadau ta buɗe babban kamfanin ta na Sadauz Home

Related Posts

Surar yaƙin jihadin Islama (Hoto daga shafin History of Islamic Wars, a Facebook)
Addini

Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka: Daga Wali Ɗanmasani zuwa jiya

June 21, 2023
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi
Addini

Baban mu Shehu Ɗahiru Bauchi ya cika shekara 98

August 2, 2022
Sheikh Ibrahim Khalil
Addini

Majalisar Malamai: Har yanzu Sheikh Ibrahim Khalil ne shugaba, inji gamayyar malaman Kano

October 12, 2021
Sheikh Ibrahim Khalil
Addini

Malamai sun bayyana tsige Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malaman Kano

October 11, 2021
Hukuncin ranar Idi
Addini

Hukuncin ranar Idi

May 12, 2021
Sama: Musulmi na sallah a Legas. A ƙasa: ƙwayoyin cutar 'Coronavirus'
Addini

Annoba, ibada da addini a arewacin Nijeriya

March 20, 2020
Next Post
Rahama Sadau a wajen gabatar da Sadauz Home ga jama'a

Rahama Sadau ta buɗe babban kamfanin ta na Sadauz Home

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!