• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

2023: Yadda ziyarar shugaban INEC hedikwatar CBN ta cire shakkun samun tangarɗar kuɗaɗen sallamar ma’aikatan zaɓe

by DAGA WAKILIN MU
February 8, 2023
in Nijeriya
0
Daga hagu: Farfesa Mahmood Yakubu ya na gaisawa da Mista Emefiele a lokacin ziyarar

Daga hagu: Farfesa Mahmood Yakubu ya na gaisawa da Mista Emefiele a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN Bankin Nijeriya (CBN) ya shaida wa Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, cewa sauya launin kuɗi ba zai shafi zaɓen 2023 ba.

Ya ce bankin zai samar wa INEC da dukkan kuɗaɗen da hukumar ke buƙata a lokacin zaɓuɓɓukan ranar 25 ga Fabrairu da na 11 ga Maris, 2023.

Gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele, ya shaida wa Yakubu cewa a ko da yaushe CBN na goyon bayan INEC ta kowane fanni domin tabbatar da cewa ta gudanar da aikin da aka ɗora wa hukumar a cikin nasara.

Ya ce: “Mu na shiga harkokin ayyukan INEC adanawa da ajiyar kayan zaɓe, har ma da amfani da motocin CBN masu sulke wajen rarraba kayan zaɓe.

Jami’an INEC da na CBN a lokacin ziyarar

“Mu na farin cikin cewa a cikin wannan kyakkyawar alaƙa tsakanin CBN da INEC, ba mu taɓa kawo wa INEC cikas ko dagula masu lissafi ba. Saboda haka ɗin ne ma ba ku gudun mu, ga shi a yanzu ma kun dawo mana a wannan zaɓen.

“Idan shugaban INEC zai tuna, lokacin da na kai maka ziyara a baya, ka tambayi yadda CBN zai samar wa INEC kuɗaɗen waje domin sayen na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS), da sauran kayan aikin zaɓe. Na ba ka tabbacin za a samar, kuma an samar ɗin.

“Saboda haka, CBN ba zai bari a yi amfani da shi ba wajen kawo wa zaɓen 2023 cikas.

“Don haka ina tabbatar maka idan ka na buƙatar takardun kuɗaɗe domin biyan motocin sufuri kuɗin su a hannu, bayan ka yi biya ta tiransifa, to CBN a shirye ya ke ya bayar.”

Tun da farko, Farfesa Yakubu ya nemi haɗin kan CBN domin tabbatar da zaɓen 2023 cikin nasara, musamman ganin yadda ake ta haƙilon ƙarancin kuɗaɗe kusa da zaɓe.

Ya ce INEC ta yi shiri tsaf domin tabbatar da zaɓen 2023 ya zama sahihin zaɓen da a tarihi ba a taɓa yin kamar sa ba a Nijeriya.

Loading

Previous Post

INEC ta fara horas da ma’aikatan wucin-gadi miliyan 1.2 domin aikin zaɓen 2023

Next Post

Yadda taron tunawa da Mahmoon Baba-Ahmed da ƙungiyar Alƙalam ta shirya ya gudana

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Wani sashe na mahalarta taron

Yadda taron tunawa da Mahmoon Baba-Ahmed da ƙungiyar Alƙalam ta shirya ya gudana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!