JARUMIN barkwanci, Aliyu Muhammad, wanda aka fi sani da Ali Artwork ko Maɗagwal, ya bayyana dalilin komawar sa Kwankwasiyya bayan lashe zaɓen Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Jihar Kano.
Ali Artwork dai ya bar tafiyar Kwankwasiyya wata huɗu da su ka gabata, wanda a wancan lokacin ma ya faɗi dalilin sa na yin hakan.
A hirar da ya yi da mujallar Fim, jarumin ya ce, “Mutane ne ba su gane ba. Ni yanayin siyasa ta, ba irin yadda mutane su ka ɗauke ta ba ne. Ni ba na siyasar gaba, ba na siyasar in zagi can, in koma can.
“Dukkan su waɗannan jam’iyyun, kamar yadda na ke ‘star’ ne ni, a kowace jam’iyya ina da magoya baya da masoya da su ke so na. Na yi bidiyo na faɗa cewa duk wanda ya ci zaɓe zan taya shi murna, kuma in ya ce zo mu yi tafiya, zan bi shi don in yaɗa manufofin sa. Wannan shi ne tsari na tun kafin a shiga zaɓe. Abin da na faɗa kenan.”
Ya ci gaba da cewa, “Wancan karon na bar Kwankwasiyya saboda an ɓata min rai, yanzu kuma sun ci zaɓe na dawo in ci gaba da ba da gudunmawa ta. Wannan shi ne kawai.”
Game da hantarar da wasu daga cikin masoyan Kwankwasiyya su ke yi masa, musamman da su ke nuna ba su yarda da shi ba, jarumin ya ce, “Tun da ake magana, ka ji wani babba a Kwankwasiyya ya fito ya yi magana? Yawancin su mutanen gari ne, kuma ba su da wata alaƙa da siyasar sosai, kuma su na maganganun ne ba su san ya siyasa ta ke ba. Amma su jagororin maraba su ke yi da ni da na’am, musamman ma shi mai girma gwamna. Duk sun ji daɗi da dawowa ta.”
Ali ya ƙara da cewa, “Ni duk inda aka kira ni, zan tafi. Ina da masoya a PDP, APC, APGA da NNPP. Kuma duk su na so in ba su gudunmawa. Menene gudunmawar? Su na so in tallata ɗan takara, in yaɗa manufofin sa.”

Da mujallar Fim ta tambaye shi matsayin sa a wurin su Gwamna Ganduje a yanzu, sai ya ce, “Duk matsayi na wurin su kamar yadda mu ka ƙulla alaƙa ta mutunci da zumunci, ta na nan. Don ni ba na irin wannan rayuwar, in na yi mu’amala da mutum in yanke alaƙa da shi. Sai dai in kai ka ce ka yanke alaƙa da ni sai in kama kai na. Amma mu na gaisawa, mu na zumunci, kuma haka duka siyasar Nijeriya ya kamata ta koma.”
An ce Ali Artwork, ya ce jifar sa aka yi, ya sa ya bar Kwankwasiyya. Shin hakan ne? Ali ya ce, “Da na ga sun matsa min ne da maganganu, ka san ni mutum ne mai wasan barkwanci da dariya da raha, wannan dalilin ya sa na ɗan yi rubutu, wanda ya sa wasu daga cikin su su na ta dariya, su na cewa na ga an ci zaɓe ne na dawo kwaɗayi.
“Kuma wani abin daɗin daɗawa, ni ba na zuwa gidan ɗan siyasa, duk gidan ɗan siyasar da ka gan ni, nemo ni ya yi ko ya sa yaran sa su kira ni ko kuma ya ɗaga waya da kan shi ya kira ni. Amma ni ba zan je gidan ɗan siyasa don ya ba ni wani abin duniya ba. Ina da sana’a, ina neman kuɗi, ni ba wai kwaɗayi ko wani abu ba ne, kawai dai ni na zaɓi in yi harka ta da kowa.
“Ni ba zan maƙale wa ɗan siyasa ɗaya ba. In ka maƙale, ƙarya ke biyo baya. Ka zo ka tallata ɗan siyasa, menene naka na ce masa ka na tare da shi ɗari bisa ɗari? Ka ga ka masa ƙarya kenan, dole in ka bar shi zai ji haushi. Kawai ka same shi, mu sana’a mu ke yi, ka tallata shi ya biya ka. Tunda ba taimakon sana’ar taka zai yi ba, don me kai za ka taimaki tashi ta ci-gaba kai ba zai taimaki naka ba?
“To ni yadda na zaɓi na yi siyasa na kenan, wanda na riga da na faɗa wa mutane ni in ba takara na fito ba, wai in tsaya wa jam’iyya ɗaya, wallahi ba zai yiwu ba. Sai dai in takara na fito ko kuma wani babban muƙami aka ɗauka aka manna min wanda zan amfana, ni ma in amfanar da al’umma. Wannan shi ne.”