• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 19, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

by IBRAHIM SHEME
December 7, 2023
in Mawaƙa
0
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

Alhaji Muhammadu Gao Filinge da jama'ar sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A shahararriyar waƙar nan ta “Najeriya Da Nijar” wadda marigayi Alhaji Muhammadu Gao Filinge ya yi, ya na ambatar waɗansu shaihunnai guda biyu, wato Sheikh Usman Ɗanfodiyo da Sheikh Mahaman Dioɓɓo. A yayin da yawancin mu mun san wanene Ɗanfodiyo, ba kowa ba ne zai ce maka ya taɓa jin sunan ɗaya shehin in dai ba a wannan waƙar ba. A wasu wurare ma da na ga an rubuta waƙar, ko sunan shi ba a rubuta daidai ba. Gao Filinge ya kira shi da “Mamman Jaɓɓo”, wanda daidai ne da Hausar mu amma ba a rubutun Hausar Faransa ba. Ban tabbatar ba, amma ina jin ko a Nijar ɗin ma ba a cika maganar shi ba. Allahu Akbar!

A gani na, ya kamata a san wanene Alfa Mahaman Dioɓɓo jikan shehin malami Boubacar Salihou, a yi maganar shi sosai. Dalili shi ne shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen jihadi a wancan zamani, kuma ya assasa gari da masarautar Sayi, wadda ta kasance wani muhimmin yankin Daular Usmaniyya shekaru ɗari kafin zuwan Turawa.

Ɗaya daga cikin mugun gado da mu ka yi daga mulkin mallaka shi ne zuwan Turawa ya datse hulɗar Sakkwato da Sayi, sakamakon yadda ya datse kudancin Nijar da arewacin Nijeriya ta fuskokin zamantakewa, siyasa, tattalin arziki, da al’adu, ya mayar da mu bare ga junan mu har ta kai ga kwanan baya aka riƙa kumfar baki kamar za a haɗa mu yaƙi.

Ga dai abin da Muhammadu Gao Filinge ke cewa a riwayar da ya saƙa cikin wannan fitacciyar waƙar tasa:

JAGORA:

Amma ku bari ina hwaɗa maku ko mig gama, 

Najeriya da Nijar daidai duka.

AMSHI:

Waɗansu waliyyai da Jallah yay yi cikin duniya:

Mahaman Dioɓɓo su da Usumana na Hodiyo,

Sun taso su na cikin yawon duniya, 

Mahaman Dioɓɓo yats tsaye Sayi da martaba, 

Shi kau Usumanu Shehu has Sakkwato can shi ke, 

Amma duk cikin dare ɗai haɗuwa su kai su na hirad duniya, 

Roƙon Allah su kai shi taimaki dud duniya, Musulmunci shi yawa, 

Najeriya, Najeriya, Najeriya da Nijar daidai su ke. 

JAGORA:

Mahaman Dioɓɓo su da Usumanu bin Fodiyooo…!

GABA ƊAYA:

Ɗiyan uba da uwa ɗai su ke. 

AMSHI:

Allah ya haɗa mu tun hwarkon duniya, 

Kowac ce zai raba mu mun san ƙarya shi kai, 

Najeriya, Najeriya, Najeriya da Nijar daidai su ke.

Loading

Tags: ƊanfodiyoGano FilingeMahaman DiobboNijarNijeriyatarihi
Previous Post

Na cika shekara 30 a yau – Rahama Sadau

Next Post

Shirin Wayar Da Kai: Minista ya kafa kwamitin tsara daftarin cusa ɗa’a, kishin ƙasa da kyawawan ɗabi’u

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita
Mawaƙa

Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita

December 3, 2023
Next Post
Nijeriya ta tabbatar wa Amurka da ci gaba da yin riƙo da ‘yancin ‘yan jarida

Shirin Wayar Da Kai: Minista ya kafa kwamitin tsara daftarin cusa ɗa'a, kishin ƙasa da kyawawan ɗabi'u

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!