JARUMI a Kannywood, Haruna Shu’aibu, wanda aka fi sani da Ubalen Danja, ya samu ƙaruwar ɗa namiji.
Maiɗakin sa, Malama A’isha, ta haihu da misalin ƙarfe 9:30 na dare a wani asibitin kuɗi mai suna Nana A’isha da ke unguwar Tudun Nufawa, Kaduna.
Kamar yadda ya zama al’ada a wannan zamani, ba a jira sai bayan kwana bakwai a raɗa wa jariri suna ba, don haka Ubale ya raɗa wa ɗan sa Musa, wanda za a rinƙa kira da Farhan.
Musa shi ne ɗan Ubale na biyu.
Ubale yana ɗaya daga cikin yaran fitaccen jarumi Sani Musa Danja.
Allah ya raya Musa, ya kuma albarkaci rayuwar sa.