YUSUF Furodusa ya daɗe ana damawa da shi a cikin harkar fim, inda ya yi finafinai masu yawa tun a shekarun baya. Sai dai a yanzu an fi sanin sa a matsayin jarumi a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar talbijin ta Arewa 24.
Mujallar Fim ta tattauna da shi a matsayin sa na ɗan fim wanda ya ga jiya kuma a yanzu ake damawa da shi.
Tun da farko sai da Alhaji Yusuf ya yi lissafin irin cigaban da ya samu a harkar fim daga farkon shigar sa zuwa yanzu, ya ce: “To ina godiya ga Allah da ya kawo ni zuwa wannan lokacin, kuma a cikin harkar fim duk wanda ya san ni ina matsayin furodusa ne; sama da shekara ashirin ina yin fim nawa na kai na. Kuma alhamdu lillah fim ya yi mana komai, ya yi mana gida, ya yi mana mota, ya kai mu Makka, ya yi mana abubuwa na alkairi da ba za su lissafu ba.
“Kuma mu na godiya da har yanzu ba mu daina fim ba, kuma ba mu daina ci a cikin sa ba tunda ina yin wani aikin fim ana biya na, don ni na ke biyan ma’aikatan fim ɗin ‘Rayuwar Duniya’ na Tauraruwa TV kenan.”
Yusuf ya na kuma fitowa a diramar nan ta Arewa 24 maisuna ‘Daɗin Kowa’. A kan wannan shirin, ya ce, “Yau kusan shekara goma ina tare da su. Kuma a cikin ‘Daɗin Kowa’ sai cigaba ma da na ke samu a yanzu. Don kwanan nan ma an ƙara mani kuɗi a kan yadda ake biya na.
“Don ni jarumi ne a ‘Daɗin Kowa’. A baya ni na ke rol ɗin da Tsalha ya ke yi na munafinci, duk wanda ya kalli ‘Daɗin Kowa’ tun daga farko ni na ke rol ɗin Bukar, a matsayin da aka sa Tsalha ya ke yi na munafinci, daga baya har na zo ina soyayya, da wasu abubuwa. Duk wani waje da ake neman labari ni ake nema, sai daga baya kuma marubutan su ka canza ni na koma mai sayen kayan sata.
“Don haka ni a yanzu ina alfahari da Arewa 24 ina alfahari da ‘Daɗin Kowa’ saboda a rayuwa ta ban taɓa yin fim da na samu kuɗi kamar ‘Daɗin Kowa’ ba, domin shi ne ake dunƙule mini kuɗi na je na biya buƙatu na.”
Shin ko Yusuf ya na shirya fim ko kuwa dai ya na nan a matsayin jarumi? Amsa: “To ai ni har yanzu ban daina furodusin ba. Don ban daɗe ba na yi wani fim, ‘Ladi ‘Yar Talla’. Nawa ne na kai na. Sannan bayan shi na yi ‘Laila’, duk na zuba kuɗi na yi.”
Furodusa ya faɗi dalilin da ya sa ya rage zuba jari wajen shirya fim. Ya ce, “Yanzu abin da ya sa mu ka rage saka kuɗin mu, ba riba mu ke ci ba. In da da ne na yi ‘Ladi ‘Yar Talla’ sai ka ga na samu miliyoyi, amma a yanzu saboda harkar onlayin sai ka ga mu na yin fim ɗin ne don sha’awa.”
Shin wace riba ake samu yanzu idan an shirya fim don sakawa a onlayin? Alhaji Yusuf ya ce: “Har yanzu ni dai ban fara cin gajiyar abin ba. Ina saka kuɗi na ne ba ina samun riba ba. Ko a yanzu ina yin wani fim mai dogon zango mai suna ‘Halal’, wanda na ke yi a kan maciya haram, amma ba wai ina yi don na samu kuɗi ba sai don na kai saƙo na samu lada a kan illar cin haram da illar kawo wa iyalai haram.
“Harkar fim a yanzu gaskiya a cikin ɗari bai fi a ce mutum biyu (su ka ci riba) ba, a cikin dubbai sai dai ka sa bai fi mutum hamsin ba. Don haka maganar gaskiya ba a samun kuɗi a cikin harkar fim.
“Ni na faɗa kuma ina da jari, ko yanzu idan na ga ana samun kuɗi a fim to zan saka kuɗi na. Amma ban ga ana samu ba. Sai dai ka je ka yi ta sakawa a YouTube ka na yi wataƙil ka yi nasara ko kuma ka yi asara.
Shi ne abin da ya ke faruwa yanzu a harkar fim.
“Kuma ba na yin nadama a kan magana ta; harkar fim ba a samun kuɗi a yanzu. A da an yi fim an samu kuɗi, amma yanzu ba kuɗi ake samu ba. Kawai dai sha’awa ce ta ke kawo wasu, kuma sha’awa ce ta zaunar da wasu a yanzu.”
Mujallar Fim ta tambaye shi hanyar da za a bi a farfaɗo da harkar fim a yanzu. Sai ya amsa: “To kawai dai wanda ta ke yi da shi ya ci gaba, don duk wanda ya ke samun kuɗi a yanzu mu na jin daɗi, mu na taya shi murna da fatan alkairi. Kawai dai in mun zo a matsayin mu na waɗanda su ke yin fim mu ke da sha’awa za mu iya ba ka gudunmawa, shi ya sa a yanzu ma wasu abokan mu su kan kira mu mu yi musu aikin amma ba biyan mu su ke ba, don in ka ce za ka biya to fasawa za ka yi, ba za ka ci riba ba. Don ina yi kuma ina ganin yadda ake yin fim ɗin.
“Ko a yanzu na kashe kuɗi na yi album na waƙa, amma sha’awa ce ba don na samu kuɗi ba. Da man asalin fim sha’awa ce ta ke kawo ka, daga nan sai ya zama sana’a. To kamar yadda mu ka fara da sha’awa kuma ya zo ya zama sana’a, to yanzu da babu kasuwancin sai ya koma sha’awa a gare mu. Don in ban da Arewa 24 da su ke biya na babu wani fim da na yi da na ke samun kuɗi.
“Don haka ba za mu raina fim ba, ba za mu raina sana’ar fim ba, kuma ba za mu zagi fim ba, duk wanda zai zagi fim ma ba ma tare da shi, don fim ya biya mu.”