ALHAMDU lillah! Cikin yardar Allah, lokacin auren Editan mujallar Fim, Abba Muhammad, wanda aka fi sani da Abba mujallar Fim, yi.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa Jamila Ibrahim Dassi a ranar Juma’a, 4 ga Yuni, 2021 a masallacin Juma’a na Sheikh Jafar Mahmud Adam da ke Unguwar Dosa, Kaduna.
Kafin ranar ɗaurin auren, akwai shagulgula da za a gudanar kamar haka:
* Litinin, 31 ga Mayu – Ranar Ƙauyawa (Kauye Day).
*Talata, 1 ga Yuni, – Wankan Amarya (Bridal Shower), inda za a gudanar da tarukan a gidan su amaryar da ke Legistilative Quarters, Unguwar Dosa.

* 2 ga Yuni – Gasar ƙwallon ƙafa tsakanin ‘yan gidan su ango da kuma na gidan su amarya, a filin wasa na Ahmad Musa da ke Sabon Hanya, Kamazo, Kaduna, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
* Alhamis, 3 ga Yuni – Kamu a Legislative Quarters.
* Juma’a, 4 ga Yuni – Bayan an ɗaura aure, za a yi bikin Ranar Iyaye Mata (Mother’s Day), a gidan su amaryar.
* Asabar, 5 ga Yuni – Buɗar kai a gidan iyayen ango da ke Sardauna Crescent, Kaduna.
Allah ya bada zaman lafiya, amin.