DA alama dai mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala ya zama mazari ba a san gaban ka ba a fagen waƙa ta yadda duk inda ya sa gaba sai yanayin ya dace da shi. Shi mawaƙin fada ne, mawaƙin siyasa ne, mawaƙin ‘yan kasuwa ne, baya ga kasancewar sa mawaƙin faɗakarwa.
Wani salo da mawaƙin ya yake da shi wanda ya bambanta shi da sauran mawaƙa shi yanayin waƙar da ya ke yi da kowane salo ba ki. Kamar yadda ya yi waƙa da kukuma, ya yi da tafi, ya yi da bandiri.
A ‘yan kwanakin nan sai aka ji shi ya fitar da wata sabuwar waƙar da kuntigi.
Mujallar Fim ta tattauna da Ala don jin yadda alaƙar sa ta kasance da kiɗan kuntigi da kukuma da ma sauran kayan kiɗan da ya ke amfani da su.
A amsar sa, Ala ya fara da cewa: “To ni marubucin waƙoƙin ne wanda na ke rubutun waƙoƙi a rubuce sannan kuma sai na karanta. Kuma wannan wani tsari ne da masana suka tabbatar mana da cewa mu makaɗan baka ne ko marubuta waƙoƙin baka. Sannan kuma wasu manazarta sun hukunta mu a kan marubuta waƙoƙi na zamani, saboda haka sai ake kallon mu a matsayin makaɗan baka ko mawaƙan baka na zamani.
“To, inda mu ka faɗa da daman aiki ne na manazarta, wanda ni kuma abin da na ke so mutane su gane, tsawon lokaci ni na fara waƙoƙin nan ma a daɓe ne.
“Kamar misali idan aka yi duba zuwa 2007 a lokacin Malam Ibrahim Shekarau ya na gwamnan Jihar Kano, an ƙaddamar da wani shiri na Adaidaita Sahu da aka ƙaddamar da shi a Ƙananan Hukumomi 44 na Jihar Kano. To, a lokacin muna bin Sarkin Kano mu na yin waƙar, amma babu kiɗa sai tafi.
“Misali, irin waƙar ‘Rayuwa a Duniya Tana Ban-tsoro’ da makamantan su, irin su ‘Sababin Mutuwar Aure’, su na ke yi a lokacin da wasu waƙoƙi na yabo, duk a ƙarƙashin Hukumar Adaidaita Sahu.
“To, ka ga mu na yin waƙar ma haka da ka sai dai mu haddace mu karanto baitukan. Wannan ya sa ni na ke ɗaukar kiɗa da waƙa a matsayin wani abu da zai ja hankali, ko an yi shi da gwangwani, ko kwalba, kukuma, lalajo, amada, kuntigi. Saboda haka duk abu ɗaya ne.
“Abin da zai jawo hankali ne. Saboda haka idan na tsara waƙar da na ga za ta yi tsari da kukuma, da ita zan yi.
“Kamar misali shawarar da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya ba mu, ya ce za a yi taron tunawa da Ɗanmaraya Jos, me zai hana mu ɗauki wata waƙar sa mu yi haɗaka don mu yi masa ta’aziyya? Wannan ce ta sa mu ka shirya waƙar ‘Mai Akwai Da Babu’, waƙar Ɗanmaraya ce mu ka yi haɗaka ni da Fati Nijar.
“Ka ga waƙar ta kuntigi ce, amma saboda ɗan Garba Sufa ya na tare da mu a lokacin sai mu ka buga mata kukuma mu ka haɗa da kayan kiɗa na zamani, kuma ta zo ta yi fice, duk da asalin waƙar ta mai kuntigi ce kuma da kuntigi aka yi ta.”

Dangane da sabuwar waƙar da ya yi da kukuma, Ala ya yi bayanin cewa: “To, shi abin da ya faru, Babangida Kakadawa shi ne ya kawo mini ziyara, a lokacin har ma na ke cewa za a yi bikin ‘ya’ya na. Ya ce zai yi mini waƙar talla don a tallata bikin. A nan ya yi ta. Sai kuma na ce da shi to ni ma sai ka dan yi mini wasu kiɗoɗi haka da zan yi amfani da su na yi wasu waƙoƙi na daban.
“To wannan ya sa aka ji ni da waƙar kukuma har na yi wa Aminu Ado Bayero waƙa. Saboda haka mu na yi mu na saka kalangu, da sauran kayan kaɗe-kaɗe, amma dai ba mu cika bai wa kiɗa muhimmanci ba. Saboda ba da kayan kaɗe-kaɗe mu ka taso ba a tsarin rubuce-rubucen waƙoƙin mu.
“Asalin ma ni ina kallon su Mudi Sipikin ne, su Mu’azu Haɗeja. Don ka ga waƙoƙin su da aka yi su a kan ma’auni na baharin waƙa, to amma ina iya ɗaukar su na ɗora su a kan kiɗa na zamani kuma su tafi a hakan.
“Misali kamar waƙar Muhammadu Uba Adamu, akwai waƙoƙin sa waɗanda ba juya su na yi ba, yadda su ke haka na ɗauke su, sai dai na gabatar da su cewa wannan waƙar ba tawa ba ce, ta Muhammadu Uba Adamu ce, ni biyawa na yi na kai su situdiyo aka ɗora musu kiɗa; wajen waƙoƙi huɗu na ɗauka.
“Sai kuma waƙar Mudi Sipikin da na ɗauka wadda ita haka na karanta ta gayan ta a situdiyo.
“A yanzu ma akwai waƙoƙin Sa’adu Zungur da na ke so na ɗauka na karanta na ɗora musu kiɗa, kamar dai yadda na yi wa waƙoƙin Abubakar Ladan wanda su ma haka ya ke yin su babu kiɗa ba komai. Amma sai na ɗauki waƙar ‘Haɗa Kan Afirka’ ba tare da na ƙara ko na canza wasu baituka ba. Haka yadda yake yi ni ma na bi na rera.
“Saboda haka, mu mu shiga situdiyo mu taɓa wani abu na kiɗa ko jita, duman girke ko jarka ce za mu buga ta bayar da ma’ana duka.
“Mu abin da mu ka ɗauki kiɗa kawai ƙararrawa da zai jawo hankali don mu isar da saƙon da mu ke so mu isar, shi ya sa duk wani kiɗa da zai ja hankali ya yi mana daɗi, musamman kaɗe-kaɗe na gargajiya da mu ke so mu dawo da su, don a san mu na da irin sauti namu na Hausawa, kada ya ɓace.
“To, wannan ya na daga cikin abin da ya sa na ke ɗauko su na ke yin amfani da su, da ma kare-karen harshe wanda daga mutum ya ji ya san ba wani Balarabe ko wani Ba’indiye ne zai yi waƙar, don haka mu ka fi ba da ƙarfi a kan al’adar.
“Don haka ni zan ci gaba da yin haka domin inganta rayuwar mu ta gargajiyar Hausawa yadda za farfaɗo da al’adar.”