FITACCEN mawaƙin siyasa, kuma shugaban ƙungiyar 13X13, Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara), ya bayyana dalilin sa na shirya taron saukar Alƙur’ani da yi wa ƙasa addu’a domin matsalar tsaro da ta ke fama da ita.
A yayin da ya ke yi wa manema labarai ƙarin bayani game da taron, Rarara ya ce, “Wannan taro da ke magana, ni shugaba ne na ƙungiyar 13X13, ma’ana President, amma taron in aka duba za a ga ba ‘yan 13X13 aka ce ba, mun ce mu kira mutane ne waɗanda su ke faɗakarwa, ma’ana ‘yan fim da kuma alarammomi ‘yan’uwa na mu zo mu karanta Alƙur’ani a kan waɗannan abubuwa da su ke faruwa a ƙasa, musamman arewacin ƙasar nan.
“To, a gaskiya mu na neman addu’o’in mutane, kuma dama aikin 13X13 ta nuna wa mutane abin da ya kamata su riƙa yi.
“Abin da ya sa mu ka shirya wannan taro, saboda mu na buƙatar addu’a, aikin finafinai da aikin waƙoƙi babu abin da ya kai su son zaman lafiya, saboda idan babu zaman lafiya abin ba yiwuwa zai yi ba, duk abin da ake tsammani ba zai yiwu ba.
“Don haka zaman lafiyar mu ke so, musamman zaman lafiya a cikin mu, zaman lafiya a ƙasar mu, musamman zaman lafiya a masana’antar mu.
“Saboda abubuwa su na ta faruwa, wanda ko da ko babu, to da mu a ciki. Domin wani ke ɗaukar abin ya yaɗa, wanda bai sani ba in ya gani abin ya ɗaga masa hankali. Kuma ba su na yi ba ne don a gani a yi addu’a, sai don su ɗaga wa mutane hankali.

“Kuma wannan abu duk duniya ake yi, amma mu ƙasar mu mu ke gani ko garin, ko gidan mu. To, ta nan ya kamata mu fara duba ta ina ne za mu fara gyara wannan abu tukuna, sai na ga lallai sai gyaran ya fara daga cikin mu, shi ya sa na shirya wannan taro.
“Kuma da ma abin da ya kamata mu yi kenan, gida-gida, masallatai-masallatai, coci-coci da duk wani wuri da ya kamata a roƙi Ubangiji don ya kawo mana ƙarshen wannan abu. Shi ya kamata mu zauna mu yi.”
Shin ko Rarara ba ya tunanin mutane za su ce kura ya rufo da fatar akuya, kawai ya shirya wannan taro ne saboda ɗan takarar sa Bola Tinubu?
Sai ya amsa da cewa, “A’a, mu ai yanzu maganar ƙasa mu ke yi, ba maganar ɗan takara mu ke yi ba. In aka ce maganar ƙasa, ana maganar abin da zai raya ƙasar ne baki ɗaya, sai wannan ƙasar ta gyaru sannan Bola Tinubu zai ce ya na takara ko wanin sa ya ce ya na takara.
“Saboda haka, mu yanzu duk mai tallar Bola Tinubu kamata ya yi a ce ya yi addu’a, zaman ƙasar nan lafiya shi ne zai taimaki duk siyasar da za a yi. Don haka babu maganar Bola Tinubu ko wani a gefe ba. Wani ma zai ce shugaban ƙasa, duk ba wannan ba ne.
“Mu idan shugaban ƙasa zai yi nashi, jami’an tsaro su yi nasu, to mu ma akwai rawar da za mu taka. Maigida ma wanda ya ke shi da matan sa akwai rawar zai taka, tunda kai ka ce mulkar ka ake yi, amma ba ka yarda ana mulkar ka ba. Don yanzu in an ce ka kwana bakwai ba ka fita ba, cewa za ka yi babu wanda ya isa.
“Ya kamata mu gane wannan abu duka sai mun haɗu, mu taimaki jami’an tsaro da ‘information’, mu taimaki kan mu in jami’an tsaro su ka ce mana mu yi kaza mu yi, lallai wannan abu za mu taru mu kai ƙarshen waɗannan abubuwan.
“Amma duk abin da za mu yi, wani zai ce ne mun yi don wane. Mu Alƙur’ani ne mu ka ce a karanta a yi addu’a, ba ji aka yi mun saka kiɗa ana cewa ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ ba. Mun ce a karanta Ƙur’ani, don ƙasar mu ta samu zaman lafiya.
“Kuma duk wanda aka gani a nan, mutane ne da su ke ɗaukar abu su na ɗorawa a kafafen sada zumunta miliyoyin masoyan su su na gani, kuma su na koyi da su. To yau mun ce a karanta Alƙur’ani, babu wani abu da babu maganin sa a ciki, shi ya sa mu ka taru a nan.
“Kuma musamman mu ka kira dattijai mutanen mu na cikin masana’antar nan mu ka ce su zo za mu faɗakar da mutane a kan abin da ya fi dacewa, a yanzu abin da Nijeriya ke buƙata shi ne mu riƙe addu’a.”

Wannan taro dai sama da alarammomi 200 ne su ka yi karatun, a cikin su har da shi kan shi Daudan. Kuma sauka goma sha tara aka yi.
Bayan an idar da saukar Alƙur’anin ne kuma sai aka shiga yin addu’o’i.
An yanka raƙuma har biyu domin yin sadaka, kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito a labarin taron na farko.
Haka kuma an raba kuɗi ga dukkan waɗanɗa su ka halarci taron.

