MATASHIN jarumin Kannywood, Sabi’u Muhammad Gidaje, ya bayyana rashin samun ayyuka a masana’antar Kannywood sosai ne ya sa ‘yan fim su ke kafa ƙungiyoyi don yin tafiyar siyasa baki ɗaya, maimakon tafiya ɗaiɗai.
A hirar sa da mujallar Fim, Gidaje ya ce samun kutsawa cikin harkar siyasa “babbar nasara ce” ga ‘yan fim.
Ya ce: “Abin da ya sa na ce haka shi ne masana’antar mu a yanzu kowa ya san halin da ta ke ciki. Babu ayyuka sosai. Na tabbata wani yanzu ya daɗe bai yi aikin fim ba, kuma bai shigowa cikin ‘yan fim don ya na ganin babu abin da zai yi idan ya zo.
“To, yanzu kuma ga shi mu na tunkarar siyasa. Kamar yadda kowa ya sani, ‘yan fim da mawaƙa mu na ba da gudunmawa matuƙa a duk lokacin da aka kaɗa gangar siyasa. A baya mu kan yi aiki ne ga ɗan siyasa ba tare da ƙungiya ba, duk abin da mu ka samu babu wanda zai sani ko a ce an raba da wani.
“A matsayi na na ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin ‘Gidaje Films and Musical Studio’, sai na ga ya dace a ce mun kafa ƙungiya domin ciyar da abokan sanar mu, yaran da ke ƙarƙashin mu da kuma al’umma baki ɗaya gaba.
“Wannan dalili ya sa mu ka ga ya dace mu kafa ƙungiya domin a gudu tare a tsira tare. A yanzu haka mun bi wasu ‘yan siyasar, kuma mun fara samun alkhairin da kowa a cikin mu ya fara darawa. Haka kuma al’ummar unguwanni ma mun fara bin su gida-gida mu na raba masu abinci da sauran kayan masarufi. Sannan ƙungiya na ƙara danƙon zumunci a tsakanin mu.”
Gidaje ya yi godiya ga Allah da ya ba su dama da tunanin kafa ƙungiya su mai suna Tafiyar Al’ummar Kannywood.
Ya ce: “Sauran ƙungiyoyin su ma dukkanin ƙudirorin su kenan game da kafa ƙungiya don tafiya bai-ɗaya. Kuma duk wanda ke cikin tafiyar dole zai samu abin yi a kai a kai.”
Tun bayan kafa ƙungiyar ‘YBN Network Group’ ta Abdul Amart da kuma ƙungiyar 13×13 Movement ta su Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) aka fara samun wasu ‘yan fim da mawaƙa a Jihar Kaduna su ma sun kafa ƙungiya da za ta riƙa tunkarar ‘yan siyasa a maimakon mutum ya tafi shi kaɗai.
A hasashen masu lura da al’amuran yau da kullum na Kannywood, waɗancan manyan ƙungiyoyin ne su ka sa su ma ƙananan su ka yi koyi da wannan hoɓɓasa don ganin su ma sun samu karɓuwa. A ganin su, hakan wani sabon tsari ne da zai samu abin da ake so. Kuma su na ganin yadda manyan ƙungiyoyin su ka samu karɓuwa a wurin ‘yan siyasa.
A baya, kowa ya san cewa ya na da wuya ka ga wani mawaƙi ko ɗan fim ya kwashi tawaga zuwa wurin wani ɗan siyasa ko babban mutum da sunan ƙungiya. Sai dai kawai mutum ya yi ayyukan sa ya tafi shi kaɗai ko kuma ya samu wasu mutum biyu zuwa uku a matsayin ‘yan rakiya, ko kuma idan mawaƙi ya yi waƙa ga wani Basarake ko ɗan siyasa, sai ya ɗauki tsala-tsalan ‘yan mata biyu su yi masa rakiya don ya cimma abin da ya tafi nema. Haka ya zama ruwan dare game duniya, har in mawaƙi zai kai waƙa dole sai ya tafi da ‘yan mata, in kuma ba haka ba ba zai samu abin da ya ke so ba, in kuma ya samu ba zai taka kara ya karya ba. Amma in da ‘yan mata ya je, albarkacin su sai ya samu abin da bai taɓa tsammani ba, duk da cewa a wasu lokutan a kan samu matasala tsakanin ‘yan matan da iyayen gidan nasu da su ke yi wa rakiya.
Matsalar ita ce yawanci matan idan aka yi irin wannan tafiyar da su su kan samu damar ƙulla alaƙa da wanda aka je wurin shi tare da su. Har ‘yan matan su kan fi samun alheri fiye da wanda ya kai su.
A wannan gaɓar wasu ke ganin cewa tafiya a ƙungiyance ya fi muhimmanci da mutunci, duk da cewa a tafiyar ƙungiyar ma dole sai an saka mata a ciki. Amma dai za a fi samun sauƙin irin waccan matsalar da ake samu da matan.
A halin yanzu dai a Jihar Kaduna an samu ƙungiyoyi huɗu, uku a Kaduna, ɗaya a Zariya.
A Kaduna akwai 15 Artists Network, ƙarƙashin jagorancin mawaƙi Ibrahim Ajilo Ɗanguziri, akwai Tafiyar Al’ummar Kannywood, ƙarƙashin jagorancin furodusa kuma jarumi Sabi’u Muhammad Gidaje, sai kuma Zazzau G17 Artistes, ƙarƙashin jagorancin jarumin barkwanci Lawal Gundura da Mukhtar SS, wanda shi ne sakatare-janar na ƙungiyar; akwai kuma Time For Positive Change Movement (TPCM), wadda ita kuma ƙungiya ce ta ‘yan fim da kuma wasu wanda ba ‘yan fim ba, ita kuma darakta kuma mawaƙi Ibrahim Usman Muhammad (Al-Imash) shi ne sakataren ta, shugaban ta ba ɗan fim bane.
Waɗannan ƙungiyoyi sun ɗebi jama’a da dama waɗanda za su amfana daga irin ayyukan da ake yi wa ‘yan siyasa, musamman ganin an shigo lokacin siyasar, duk da cewa a irin wannan lokacin ne ‘yan siyasar su ka san muhimmancin ‘yan fim da mawaƙa.