FITACCEN jarumi kuma furodusa, Malam Ashiru Sani Bazanga (Sawun Keke), ya bayyana farin ciki kan bikin naɗa shi sarautar Kogunan Ɗanja da za a yi a ranar Asabar mai zuwa, 18 ga Yuni, 2022, a fadar Sarkin Kudun Katsina da ke garin Ɗanja a Jihar Katsina.
Sarkin Kudun Katsina, Hakimin Ɗanja da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja, Alhaji M.T. Bature, shi ne zai naɗa shi tare da wasu manyan mutane da misalin ƙarfe 10:00 na safe.A hirar sa da mujallar Fim, Bazanga ya ce tarayyar sa da Sarkin Kudu ɗin ce ta sa aka ba shi wannan sarauta, ba nema ya yi ba.
Ya ce, “Domin shi da karan kan shi tunanin shi ya ba shi, bayan ya shekara 30 a kan karagar mulki ba tare da duk waɗannan naɗe-naɗen ba, sai dagatan sa waɗanda su ke kusa da shi su ka matsa masa da ya yi ƙoƙari ya yi irin wannan naɗin. Sai Allah bai sa hankalin sa ya yi wajen ba, kuma da ya zo ya yarda zai yi bikin cika shekara talatin a kan gadon mulki, wanda a ranar 4 ga Yuni, 2022 ya cika shekara talatin ɗin cur.
“Saboda abin ya zo a takure da batutuwan zaɓuɓɓukan ‘yan siyasa, shi kuma waɗanda ya yi tunanin ya naɗa duk ‘yan siyasa ne, wannan ya sa ya ɗage bikin zuwa ranar da za a yi wannan naɗi.
“Amma tsakani da Allah, ni tarayya ce da mutunci da girma da girmamawa ta sa aka ba ni sarautar, ba don na nema ba.”
Dangane da yadda ya ji a ran sa a kan wannan sarauta da za a yi masa, Bazanga ya ce, “Alhamdu lillahi, sai in ce ina godiya ga Ubangiji. Ina kuma godiya ga iyaye da su ka sa mu a hanyoyin da su ka zama na girma, na mutunci, na daraja, har Allah ya sanya mu ke tare da manyan mutane.
“Kuma ina miƙa godiya da jinjinar ban-girma ga shi mai girma Sarkin Kudun Katsina, Hakimin Ɗanja, Alhaji M.T. Bature Ibrahim Nadabo.”
Ya ƙara da cewa, “Kuma ina yi Allah godiya da ya ba mu dama mu ka kawo wannan lokacin, bayan ina Ɗanmasanin Nassarawan Kaduna, wanda mai girma Sarkin Nassarawa Abubakar Adamu ya naɗa ni, kuma yau ga shi Allah ya kai mu a ƙasa ta, mahaifa ta, hakimi na, kuma hakimin farko, Sarkin Kudun farko a Jihar Katsina, Alhaji M.T. Bature, ya ba ni wannan sarauta ta Kogunan Katsina.
“Babu abin da zan ce in ban da godiya tare da addu’a, da fatan Allah ya zaunar da ƙasar mu lafiya, ya kuma albarkaci masarautar mai girma Alhaji M.T. Bature da kuma masarautar mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.”
Da ya ke tsokaci kan masu sukar ‘yan fim da maganganu marasa daɗi, sai kuma ga shi ana ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya ana ba su sarauta, sabon Kogunan ya kada baki ya ce, “Ka ga amsa ta zo a bakin ka, tunda ga shi har ana ɗauko ɗaiɗaikun mu ana naɗawa. Ka ga kenan shi kuma shi mai kalma a kan mutum, in ya ɓata ya sani, in ya gyara ya sani. Kuma duk wanda ka ga ya na zagin wani mutum ko waɗansu al’umma, waɗanda su ba su san su na yi ba, sakayya ta na wurin Ubangiji.
“Ai an yi wannan a Jihar Kano. An samu wani wanda ya zo a gwamnati ya takura wa duk masu wannan sana’ar, ya ci mutuncin mutane fiye da tunanin al’umma. A ƙarshe ya zo Kaduna don ya ci zarafin mu, ni kai na saboda baƙin cikin wannan abin da ya yi, ban san shi ba, bai san ni ba, amma na ji wai har da ni ya ke zagi ya na ci mana mutunci, na ji ba zan yarda ba, har aiki na bari saboda wannan mutumin.
“To ka ga kenan mu na da mutunci, mu na da daraja. Kuma alhamdu lillahi, sarakuna da manyan malamai sun san mu, sun san darajar mu, sun san mutuncin mu, kuma su na girmama mu.
“Ga shi nan a yanzu haka a cikin mu akwai hakimai da dama. Akwai waɗanda sarakuna ne yanzu, su ma kan su ‘yan wasan kwaikwayo ne. Misali, Sarkin Maskan Katsina, ya na cikin ‘Samanja Mazan Fama’, ai daga nan wasan kwaikwayo ya fara ko? Ka dubi ƙasar Zazzau irin su Tafarkin Zazzau, mai girma Jafaru ko? Hakimi ne yanzu. Ga su nan in za mu yi lissafi su na da yawa.
“Akwai manyan malamai ma waɗanda mu ka taso tun mu na yara yanzu sun zama wata tsiya a ƙasar nan, kuma duk mun yi wasan da su.
“Shugabanci ba irin wanda ‘yan fim ba su yi. Sai dai ban ƙi maka ba da ake cewa wake ɗaya shi ke ɓata gari. Idan a cikin mu akwai baragurbi, Allah ya shirya su, ya sa su fahimta, kuma su daina ɓata mana suna.
“Amma masu yi mana kuɗin goro ɗin nan, kuskure ne. Ni yanzu ka ga ni ai rabon da in shiga wasan kwaikwayo ban san iyakar kwanakin ba, ban san iyakar watannin ba. Amma duk inda na ji an zagi ɗan wasan kwaikwayo ko ɗan fim, sai in ji kamar an soke ni da mashi a zuciya don ka kashe ni, domin na san ba ka faɗi gaskiya ba, kuma na san ka ci mutunci, kuma na san ka zalunce mu, kuma za mu bar ka da fitowar rana da faɗuwar ta.”
Shi dai Ashiru Sani Bazanga, ɗan jarida ne a gidan rediyo da talbijin na Liberty da ke Abuja, amma ya taɓa yin aiki a gidan rediyo da talbijin na Alheri da DITV a Kaduna da Rediyon Jihar Kaduna da Rediyon Tarayyar Nijeriya na Kaduna da Muryar Nijeriya a Legas a lokuta daban-daban.
Ya yi fice ne musamman a wasan kwaikwayo na talbijin mai suna ‘Sawun Keke’ wanda aka riƙa nunawa a gidan talbijin na Jihar Kaduna a shekarun baya, sannan da harkar finafinan bidiyo ta zo kuma ya shirya finafinai da su ka haɗa da ‘Aminan Zamani’.