YUSUF Muhammad Abdullahi, wanda aka fi sani da Yusuf Lazio, ya na ɗaya daga cikin matasan mawaƙa kuma jarumai waɗanda tauraron su ke haskawa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood. Lazio ya daɗe a masana’antar, kuma ya fi ƙwarewa a waƙoƙi irin na hip-hop (gambara) amma bai yi fice ba sai a lokacin da su ka yi wata waƙa mai suna ‘Maryama’ shi da abokin sa kuma maigidan sa Umar M. Shareef.
Yusuf Lazio mutum ne mai sauƙin kai da ladabi da biyayya. Ya na da wata ɗabi’a ta kiran kowa a masana’antar da Oga, wadda ke ɗaure wa mutane da dama kai, kuma bai damu da a sama da shi ka ke ko a ƙasa da shi ka ke ba.
Wani abin burgewar shi ne Lazio ya na da mata da ‘ya, ya yi aure aƙalla zai kai shekara shida yanzu.
Mujallar Fim ta yi nasarar tattaunawa da jarumin kuma mawaƙi, ya kuma feɗe mana biri har wutsiya game da yadda ya fara harkar waƙa da fim da sauran abubuwan da su ka shafe shi.
FIM: Ka faɗa wa masu karatu tarihin rayuwar ka a taƙaice.
YUSUF LAZIO: Suna na Yusuf Muhammad Abdullahi, wanda ake kira da Yusuf Lazio. An haife ni a unguwar Rigasa, Kaduna. Na yi karatun firamare na a nan cikin Rigasa, sannan na fara sakandare na a Kano daga aji 1 zuwa 3, sannan na dawo Kaduna inda a nan na ƙarasa. Daga nan karatu na ya tsaya a nan. Bayan nan sai kuma na tsinci kai na a harkar waƙe-waƙe da finafinai.
FIM: Me ya ja hankalin ka ka shiga harkar waƙa da fim?
LAZIO: Gaskiya abin da ya janyo hankali na, ni mutum ne mai yawan kallon waƙoƙin Turanci. A can baya akwai wani mawaƙin Amerika da ya yi tashe mai suna Sisqo, sai ya kasance ni masoyin sa ne, kuma dukkan abubuwan da ya ke yi ina kwakwayon sa, kamar irin shigar sa da sauran su. Sannan akwai irin su Nelly da sauran su, duk na yi irin wannan abubuwan.
Daga nan na fara tunanin ai ana yin waƙa da Hausa, me zai hana ni ma in kwatanta yi? Allah cikin ikon sa mu ka haɗu da Umar M. Shereef, sai kuma na fara tunanin yadda za mu yi waƙa. Amma da ma can shi Umar ɗin ya iya waƙa. Sai mu ka yi wata waƙa mai suna ‘Ku Zo Mu Je Makaranta’. Wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da ya fara kai ni harkar nishaɗantarwa.
FIM: Ya aka yi ka haɗu da Umar M. Shereef?
LAZIO: Unguwar mu ɗaya da shi. Kuma shi ma bai taɓa yin waƙa a situdiyo ba a lokacin. Sannan da ma tare mu ke rayuwar. Ma’ana dai, aboki na ne tun fil’azal.
Da ya fara rubuta waƙa sai na ke ce masa ni ma fa ina sha’awar yin waƙa da sauran su. Sai ya ce mani in haka ne ai za mu iya zuwa situdiyo, kuma a wancan lokacin situdiyo ɗaya na sani a garin Kaduna. A lokacin ina da shagon aski da bidiyo kulob. Da na samu ‘yan kuɗi na kawai sai mu ka je situdiyo mu ka yi wannan waƙar ‘Mu Je Makaranta’.
FIM: Wato kenan ita ce waƙar ka ta farko?
LAZIO: Tabbas, ita ce.
FIM: Me ya sa ka ɗauki layin waƙar hip-hop maimakon nanaye irin yadda abokin ka Umar ke yi?
LAZIO: Abin da ya ke faruwa, ita waƙa baiwa ce. Kuma kowane mutum na duniya da irin baiwar da Allah ya yi masa, sai dai ya ƙi, ya hangi wani wuri. Don haka ni na duba na ga cewa ni hip-hop zan iya yi. Don haka in na ce zan shiga wancan layin ba ni da basira a kan wancan layin. Na taɓa gwadawa, sai na ji gaba ɗaya ba ta yi daɗi ba, in na saka waƙar ina saurare sai in ta yi wa kai na dariya. Shi ya sa na ga cewa ba zan iya fitarwa ba har wani ya ji. Amma idan na yi rap zan ji ina nishaɗi, kuma har ‘yan unguwar mu su kan tambaye ni ban yi sabuwar waƙa ba? Na fahimci rap shi ne layi na, shi ya sa na riƙe shi.
Kuma duk saƙon da ɗan wancan ɓangaren zai isar, ni ma zan iya isarwa. In ma budurwar ka ka yi wa waƙar soyayya, duk waƙoƙi na da su ka yi suna na soyayya ne, duk kuma gambara ne.
FIM: Bayan ‘Ku Zo Mu Je Makaranta’, wace waƙa ce ka fara yi kai kaɗai?
LAZIO: Gaskiya na manta sunan ta. Amma akwai wata waƙa da na taɓa yi wa wani ɗan siyasa da ya fito takara a unguwar mu, kuma da salon gambara na yi masa waƙar.
FIM: Aƙalla waƙoƙin ka za su kai nawa?
LAZIO: Ni a cikin mawaƙa ƙarami ne ni gaskiya. Nawa na ƙashin kai na ba za su wuce guda goma ba, amma waɗanda na yi tare da wasu mawaƙan, gaskiya ban san adadin su ba. Ka san mu a kan kira mu mu saka gambara a cikin waƙar nanayen ma. Saboda mutane da dama su na son su ga cewa sun yi waƙa da ni. Ban taɓa zuwa wani gari na dawo ba tare da na yi waƙoƙi da wasu mawaƙan ba.
FIM: Da wace waƙa aka san ka, wadda ta fitar da kai duniya ta san ka?
LAZIO: Gaskiya waƙar ‘Maryama’ ce ta Umar M. Shareef. Har bidiyon ta mun yi.
FIM: Ya alaƙar ka ta ke da Umar M. Shareef a yanzu, musamman ganin cewa ya zama ɗaya daga cikin taurarin mawaƙa da kuma jarumai?
LAZIO: Har yanzu Umar M. Shareef aboki na ne, kuma oga na ne a ɓangaren waƙa, don haka ina ba shi girma a kan haka sosai. Shi ya sa na ke ɗaukar sa maigida na. In kuma aka koma ɓangaren abokantaka kuma, babban amini na ne.
FIM: Ya aka yi ka fara fitowa a fim bayan waƙa?
LAZIO: Abin da ya ke faruwa, fim shi ne abin da na fara so a rayuwa ta. Amma a baya fim ya yi mani nisa. Amma da yake komai na tafiya da lokaci, sai da lokacin ya yi na fito na faɗa wa duniya cewa zan iya, kuma da ma shi na fi so.
FIM: Kwanan nan ka fito a wani sabon fim mai suna ‘Maya’, wanda kai ne jarumin fim ɗin. Ya ka tsinci kan ka a lokacin da aka ba ka ‘script’ ɗin fim ɗin?
LAZIO: Gaskiya na ji daɗin wannan tambayar. Wato a ɓangaren fim, mai fim ɗin ‘Maya’ shi ne jigo na a fim. A fim da aka fara gani na na fito a matsayin jarumi, fim ɗin Adam A. Zango ne. Ka ga shi ya fara sa ni a fim, har na fara ji ashe ni ma ɗan fim ne.
Da aka ce za a sake shirya fim ɗin ‘Maya’, na yi ta lissafin labarai na shi, ban taɓa kawo ‘Maya’ a ciki ba, don a tunani na ‘Maya’ ya fi ƙarfi na. Labarin fim ɗin sai wanda ya kai zai iya yin shi. Ina zaune aka ce min za a yi fim ɗin. Falah M. Shareef shi ne furodusan ‘Maya’, ya ɗauko ‘script’ ɗin fim ɗin ya ba ni, na ce masa me zan yi masa? Ya ce min ai za mu yi aikin fim ɗin ne. Na ce masa ba damuwa duk da yake a lokacin ban san cewa da ni za a yi aikin ba. A haka dai ina ta tunanin abubuwan da za a iya cewa zan yi a aikin. Abu na gaba da zan ji sai kawai aka ce min ni ne jarumin da zai ja fim ɗin. Gaskiya na ɗauka wasa ne ko kuma mafarki na ke yi! Mu ka je gaban Adamu, ya tabbatar da cewa ni ne zan ja fim ɗin. Na ce “kamfanin Adam A. Zango ne, kuma shi zai bada umarni, yau Lazio ne za a yi masa fim a kamfanin, kuma zai hau matsayin da Adam A. Zango ya taɓa hawa!” Daga nan sai na yarda cewa ni ne za a yi wa fim ɗin.
Sai kuma wani abin ya dame ni a cikin zuciya ta. Adam A. Zango ya na ɗaya daga cikin jaruman da su ka fi kowa iya fim a Kannywood, sai kuma yau ga shi ni Yusuf Lazio ne zan hau matakin da ya taɓa hawa! Wannan abin ya tayar min da hankali. Ina ta tunanin ba zan iya ba. In dai taƙaice maka labari, sai da mu ka fita aikin fim ɗin, aka yi sin ɗaya, aka yi na biyu, a na uku aka ce, “Lazio saka kaya an zo kan ka,” wallahi sai da na ji wani yarr a kai na! Daga nan na cire komai a kai na, na yarda da gaske ne za a yi aikin.
FIM: Ya ka ji a lokacin da aka sanar da kai rol ɗin da za ka hau na wani irin mutum mara mutunci, wanda har kitso ya ke yi a kan sa?
LAZIO: Na farko dai, daidai gwargwado ina ƙoƙari a cikin gayu. A fim ɗin an ce wani mutum ne wanda zai iya yin komai a kan kuɗi, kuma gaye ne. Da farko na tambayi mai fim ɗin, Adam A. Zango, shi lokacin da ya yi fim ɗin wane irin zane aka yi masa a kan sa, ni kuma ya ake so kamanni na ya zama? Sai ya ce in je in yi abin da ya fi wanda shi ya yi. Na ce masa, “In na yi kitso, ya yi?” Sai ya ce, “Shi ne kaɗai za ka yi ya fi abin da ya fi nawa.” Ɗabi’a ta ba haka ta ke ba, gaskiya. Don a yanzu normal aski ne a kai na, hasali ma a lokacin da ake ɗaukar fim ɗin tsawon kwana shida ko bakwai ban je gidan mu ba, saboda ina da ‘ya, ba na so ta gan ni da wannan kitson a kai na, haka maiɗaki na da mahaifiya ta, musamman ita mahaifiya ta ɗin ba zan taɓa bari ta gan ni da kitson ba. Sai kawai idan fim fim ɗin ya fito sai su gani; ai ba a zahiri ba ne su ka gani, a fim ne.
FIM: Waɗanne finafinai ka fito a ciki ban da ‘Maya’?

LAZIO: Kafin fim ɗin ‘Maya’, mun yi ‘Na Ladidi’, wanda shi mu ka fara yi, kuma ni ne jarumin fim ɗin. Kuma akwai Adam A. Zango a ciki, Rahama Sadau, Umar M. Shareef, Amal Umar da sauran wasu jarumai duk a ciki. Sai kuma ‘Damfara’, da sauran finafinai masu dogon zango. Yanzu haka akwai ‘script’ sun kai bakwai a wuri na.
FIM: Ya za ka yi da waƙa tunda ka zama jarumi a fim?
LAZIO: Ba zan bar waƙa ba. Ba ni kaɗai ba ne mawaƙin da ya fara haɗa fim da waƙa. A cikin su kuwa akwai Misbahu M. Ahmad, Adam A. Zango, Sani Danja, Umar M. Shareef da sauran su. Don haka ni ba zan zama na ƙarshe ba. NZi yanzu ma na fara son waƙa!
FIM: Menene burin ka game da waƙa da kuma fim?
LAZIO: Wallahi na ji daɗin wannan tambaya, gaskiya. Yawancin mu ‘yan Arewa ba mu san ɗaukaka ba. Abin da ya ke ba ni sha’awa da ɗaukaka, na ke kuma da buri a kai yanzu, ina matuƙar so in ga ina taimakon wanda bai da shi ko kuma ina fitar da mutane daga cikin damuwa.Amfanin ɗaukaka shi ne ba ka da kuɗi ma za ka yi shi. To, amma jaruman mu na Arewa, musamman mazan, kawai sun zauna ne kara-zube da cigaba ya zo masu sai waɗanda su ke kusa da su za su taimaka, da sauran su.
Gaskiya yadda na ke kallon ɗaukaka ba haka ya ke ba. Misali, yanzu akwai Umar M. Shareef ko Adam A. Zango, yanzu idan ka je ƙasar Nijar, ka samu wani ɗan ƙasar ka tambaye shi don Allah ya sunan gwamnan Kaduna? Wallahi bai sani ba. Amma da ka ce masa Umar M. Shareef ko Adam A. Zango yanzu zai fara kawo maka waƙoƙin su da finafinan su. Wannan wata dama ce da duk lokacin da ka so za ka fitar da wasu mutane a cikin damuwa. To, ni buri na kenan a harkar waƙa da fim. Ni ko ban dauwama da arziki ba, suna na ya dauwama da wannan abin.
FIM: Ka na da tunani irin abokin ka Umar M. Shareef na waƙa da mawaƙan Kudu?
LAZIO: Ni a gani na har yanzu bai fara ba ma wallahi. Saboda shi kan shi ya san na fi shi son hakan. Shi dai dama ce kawai da ke hannun sa. Ni tunani na ya wuce nan, don ba nan na ke hari ba. Ni ba na kallon wani da ya ke tunanin ya kai wani wuri a duniya da ni ba zan je ba ko ya fi ƙarfi na ba zan iya tunkarar sa ba.
Kawai abin da zan duba shi ne menene matakin tunkarar wane? Idan ba zan iya ba zan ɗauko manaja. Wani za ka ga ya na da manaja sun kai huɗu, kuma kowa da ɓangaren sa. Yanzu ko Shugaban Ƙasa za ka gani, akwai matakan da ake bi kafin a gan shi. Don haka in lokacin ya yi ina da wannan ra’ayin fiye da nashi ma.
FIM: Waɗanne irin nasarori ka samu a cikin wannan sana’a?
LAZIO: Gaskiya na samu nasarori. Babbar nasarar da na samu su ne masoya. Ya na da wuya gari ya waye wani bai kira ni daga wani gari ya ce min wane ne, ya ga abu kaza nawa ya ji daɗi. Wannan babbar nasara ce. Don haka ina alfahari da wannan nasarar.
FIM: Ƙalubale kuma fa?
LAZIO: Gaskiya na samu ƙalubale. A matakin da na ke a yanzu haka ina tare da wani maigida na, Sulaiman Sir Zeesu. Ina da sana’a manya, na yi harkar mai, a yanzu haka abokan harka ta manyan masu kuɗi ne, manyan motoci su ke hawa. Duk abin da zan yi, hankali ya na kan fim, sai na aje komai na dawo na koma ina bin Sir Zeesu, ya zama maigida na. A lokacin da ya zama maigida na, na samu ƙalubale da wallahi ina kasa barci. Mutane na zagi na har ya na dawowa kunne na. Amma kullum abin da na ke dubawa ya na ke da mahaifiya ta, mahaifi na ba shi da rai, ya na ke da shi kafin ya rasu, ya na ke da family na? Kowa ba ni da matsala da shi. Wannan ya sa ba na ɗaukar wannan abin a matsayin ƙalubale. Da ma kuma in dai ka bi hanyar nasara dole ka haɗu da ƙalubalen da ba ka taɓa samu ba.
FIM: A ƙarshe, me za ka ce wa masoyan ka?
LAZIO: Abin da zan ce wa masoya na shi ne su ƙara haƙuri. Ni Yusuf Lazio in Allah ya so ya yarda, in-sha Allahu sai na zama ɗaya daga cikin mutanen da ake kallo a duniya a wannan masana’anta. In na ce a duniya ina nufin duka ɗoka duniya ne. Don Allah su ƙara haƙuri da ni, sannan da sun ga na yi kuskure, su kira ni su faɗi, zan gyara in-sha Allahu. Ba na ƙin ɗaukar waya, akwai lamba ta a shafi na na Instagram. Ina godiya da irin ƙaunar da su ke nuna min.
