A YAU Litinin, 17 ga Yuni, 2019 mawaƙi Honarabul Abubakar Salisu (ASAS) ya shirya walimar buɗe sabon katafaren gidan da ya gina a unguwar Rafin Guza da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.
Walimar, wadda aka fara da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, ta samu halartar ’yan fim na Jihar Kaduna da dama.
Da farko Malam Abubakar Abdullahi ya buɗe taron da addu’a, sannan ya yi jawabi, inda ya ja hankali ga shi Abubakar ASAS game da ginin da ya yi, na kada wannan ya sa ya riƙa wasa da ibada, kuma ya riƙe iyayen sa hannu biyu-biyu.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah ya sa rai aka yi wa.
Haka shi ma aminin ASAS, wato Adam A. Zango, ya yi jawabi, inda ya ce, “Alhamdu lillahi! A matsayi na na abokin shi kuma yayan shi, ina murna, domin samun muhalli ba ƙaramin abin farin ciki ba ne. Ni ma na daɗe ba ni da muhalli, sai kwanan nan ni ma na mallaka. Ina yi masu fatan alheri, Allah ya ba su zaman lafiya da iyalin sa. Allah kuma Ya sa rai ka yi wa.”
Mahaifiyar Abubakar ASAS, wato Hajiya A’isha Abdullahi, da matar sa Hauwa’u Isah Sa’eed, su ma sun tofa albarkacin bakin su.
Duk da cewa abin na ’yan fim ne da mawaƙa, ba a sa waƙa ba, ƙira’a aka sa har lokacin da aka yi aka gama, sannan aka sa waƙar Adam A. Zango.
A ƙarshe, mai gayya Abubakar ASAS ya yi jawabin godiya, inda ya ce, “Yau ina cike da farin ciki da Allah ya nuna min ranar da na tare a cikin gida na. Allah ya ba kowa iko, duk wanda yake wurin nan, ya gina nashi, ni ma in je in taya su murna.
“A ƙarshe, ina yi wa kowa fatan alheri. Allah ya komar da kowa gidan sa lafiya. Na gode.”
Waɗanda su ka halarci walimar sun haɗa da Adam A. Zango, Saifullahi Ishaq (Safzor), Lawandi Wash, Ibrahim Saminaka, Umar Big Show, Kabir A. Zango, Hamisu Gwamna Jaji, Sadiq Muhammad, A.A. Rasheed Kabala, Hajara Muryoyi da sauran su.
Abubakar Salisu ASAS mawaƙi ne kuma furodusa. Kuma shi ne mamallakin kamfanin ‘Muryoyi Multimedia’.
