MAWAƘI a Kannywood, Abubakar Sani, ya bayyana cewa sababbin waƙoƙin da zai fara saki a yanzu waƙoƙi ne masu ma’ana tare da faɗakarwa kamar yadda ya saba yin su a baya.
Abubakar ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Duk da yake wasu su na ganin kamar na daɗe ban yi waƙoƙi da na saki a duniya ba, sai ake ganin kamar an daina yayi na. Amma dai na san har yanzu ana sauraron waƙoƙin da na yi na baya saboda an gan su su na da ma’ana.”
Mawaƙin ya yi nuni da yadda duniya ta sauya har abin ya riski mawaƙan Hausa. Ya ce: “A yanzu duniya ta canza, don haka dole ne mu bi yadda zamani ya zo da shi, domin kamar a baya za mu buga waƙoƙi ne a saka a fim. Kuma mu ka koma album, yanzu kuma sai mu ka koma ‘online’, don a yanzu ma da na yi waƙoƙin na fara sakin su ne a canel ɗi na na YouTube duk da yake a yanzu na sauraro na fara saki, sai nan gaba zan yi na kallon.”
Dangane da yanayin sababbin waƙoƙin nasa, Abubakar ya ce: “Album ne na shirya mai suna ‘Nahiya’, kuma na yi waƙoƙi guda huɗu ne. Akwai ‘Nahiya’ wadda waƙa ce a kan nahiyar Afrika da irin yadda mu ke fama da rashin haɗin kai da faɗace-faɗace da zaluncin shugabanni da kuma siyasar zalunci da ƙarya.
“Sai kuma waƙar ‘Mawaƙa’ da ‘Wasiyya Ta’.”

Ya yi magana a kan masu cewa an daina jin ɗuriyar sa, ya ce, “Ina kira ga masoya na da su ke zaton na daina waƙa, su sani ban daina ba, domin na sauya tsari ne. Ba na yin waƙar da yawa, saboda ku duba ku ga masu yin waƙar da yawa ai a yanzu duk an daina yayin su, don idan abu ya yi yawa to ya na isar mutane.
“Don haka ina tabbatar maku da cewa na zo da sabon salon da za ku san an samu sauyi kuma Abubakar Sani ɗin dai ya na nan a yadda ya ke.”