FITACCEN jarumi kuma mawaƙi Adam A. Zango a yau ya samu ƙaruwa da haihuwar ‘ya mace.
Matar sa, Safiyya Umar Chalawa (Suffy), ta haifi samɓaleliyar yarinyar lafiya ƙalau a asibiti a garin Kaduna.
Zango ya raɗa wa ‘yar tasu suna Furaira, wato sunan mahaifiyar sa, to amma saboda alkunya, an bai wa yarinyar laƙabin Diyanah.
Mujallar Fim ba ta gano asalin wannan laƙabi ba, amma wata majiya ta ce sunan marigayiya Princess Diana ta ƙasar Ingila ne aka sanya mata, musamman ganin cewa ita ma ya yi mata inkiya da ‘Princess’.

Jarumin ya bayyana labarin wannan sabuwar haihuwar da aka yi masa a soshiyal midiya a yau lokacin da ya wallafa hotuna biyar da bidiyo ɗaya na jaririyar a Instagram.
A sanarwar, ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allah s.w.t. Allah ya raya mana ita bisa turbar addinin Musulunci. Allah ya shirye ta, ya sa Annabi Muhammad s.a w. ya yi alfahari da ita ranar lahira.”
Ya ci gaba da cewa, “Sunan ta Furaira Adam. Sunan mahaifiya ta ne! Sunan kunya Princess Diyanah!”
Ɗimbin masoya sun taya Adamu da Safiyya murna tare da addu’ar Allah ya raya Diyanah, kuma ya albarkaci rayuwar ta.
A lissafin da mujallar Fim ta yi, ta fahimci cewa Diyanah dai ita ce ta bakwai a jerin ‘ya’yan Adam A. Zango. A cikin su akwai maza huɗu da mata uku.
Da haihuwar Princess Diyanah har an buɗe mata shafi a Instagram inda za a riƙa wallafa hotunan ta har zuwa nan gaba kamar yadda wasu ‘yan fim ɗin ke yi.

An ɗaura Zango da Safiyya ne a Gwandu, Jihar Kebbi, a ranar 26 ga Afrilu, 2019. Ita ce mace ta shida da ya aura, amma ya rabu da sauran biyar ɗin ɗaya bayan ɗaya.
Diyanah ce ‘yar Safiyya ta fari.
Allah ya raya Diyanah, ya albarkaci rayuwar ta, amin.