SHEKARA biyu bayan mutuwar auren sa na farko, shahararren mawaƙi kuma jarumin barkwanci a Kannywood, Ado Isah Gwanja, zai yi wani auren a ranar Juma’a mai zuwa.
Za a ɗaura auren sa da sabuwar abar ƙaunar sa mai suna Maryam Zubair Muhammad Paki a ranar Juma’a, 21 ga Yuli, 2023, a Masallacin Juma’a da ke cikin Jami’ar Yusuf Maitama Sule (Northwest University), Kano.
Yayan Ado Gwanja, wato Alhaji Sa’idu Gwanja, shi ne ya ba da sanarwar ɗaurin auren a guruf ɗin ‘yan fim ta ‘MOPPAN Associates’.
Amma Alhaji Sa’idu ya ce: “Idan ba a samu damar zuwa ba a yi mana addu’a, mun gode.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa, a shekarar 2021 ne mawaƙin ya rabu da matar sa Maimunatu Ɗan’auta, wadda su na ‘ya ɗaya da ita mai suna Asiya (Balaraba).
Ya zuwa yanzu dai ba mu samu labarin ita Maimunatu ta samu yin wani auren ba.