SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallahu), ya bayyana cewa hukumar sa ta kulle shagon ɗaukar hoto na ‘Celebrity Photography’, mallakar jarumi Sani Musa Danja, saboda hakan ya na cikin aikin hukumar tasa.
Bayanin nasa ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya ɓarke, musamman a Kannywood, game da wata rundunar aiki da shugaban ya kafa domin kula da wasu sana’o’i a jihar, ciki har da ɗaukar ɗaukar hoto da shagunan saida magungunan Musulunci da ake kira ‘Islamic chemists’.
Hukumar ta ce tilas su je su yi rajista da ita.
A ranar Litinin ta makon jiya ne, wato 27 ga Janairu, 2020, Afakallahu ya kafa wannan tawagar aiki mai taken ‘Idan Ba Ka Yi, Ba mu Wuri’ (KSCB Operation Team).
Kamar yadda jami’in yaɗa labarai na hukumar, Mal. Salihu Adamu Aliyu, ya rubuta a sanar da manema labarai, ayyukan wannan tawagar sun haɗa da tantancewa da tsaftace dukkan wani abu da ya shafi nishaɗantarwa.
Ya ce bayan haka, idan hukumar ta tabbatar da ingancin masu wannan sana’a ta nishaɗatarwa, za ta ba masu lasisin gudanar da ayyukan su, ba su da wata matsala da hukuma.
“Sai dai kuma duk wanda ke gudanar da sana’a ba tare da lasisi ba, wannan tawaga za ta kama tare da kulle masana’antar sa, kuma a gurfanar da shi,” inji shi.
Ya ce aikin tawagar, ba ‘yan fim da mawaƙa kaɗai ya shafa ba, domin kuwa za a taɓa kowa ne, kama daga lokeshin na ɗaukar finafinai, gidajen kallon ƙwallo, sinima, sitidiyon ɗaukar waƙoƙi, sitidiyon ɗaukar hoton kati, shagunan wanke hotunnan kati, allunan talla, gidajen dirama irin na daɓe, gidajen shagulgulan biki na zamani, shagunan masu tura finafinai a waya, shagunan magunguna irin na Musulunci, shagunan masu ɗab’i, shagunan masu saida littattafai, masu saida fosta da sauran su.
Tawagar ta fara aikin ta a yau Litinin, 3 ga Fabrairu, 2020.
Sabon shagon ɗaukar hoto na Sani Musa Danja ta na cikin shagunan da aka fara ta kan su.
Sai dai kuma al’amarin ya tada ƙura, domin kuwa mutane da dama sun faɗa wa mujallar Fim cewa ba hurumin hukumar ba ne kula da wasu daga cikin wuraren da ta lissafa, misali situdiyon ɗaukar hoton kati da shagunan magungunan Musulunci. A ganin su, ta wuce gona da iri.
To amma a hirar sa da mujallar Fim, Malam Afakallahu ya ce abin da ta kawo wannan tunanin shi ne irin waɗannan mutanen “ba su san menene dokokin hukumar ba.”
Ya ce, “Da ma hukumar ta na da alaƙa da gidajen hotuna, albums na bidiyo da kuma situdiyon ɗaukar hoto.

“Sannan hukumar ta na kula da dukkan wani abu da ya shafi hoto mai motsi da mara motsi.
“Ganin fim a harkar shi ne sai ya danne komai, abin da ake ce wa gani ya kori ji, don haka irin ƙarfin fim ne ya sa wasu abubuwan na hukumar sai a ga cewa me ya haɗa Hukumar Tace Finafinai da kaza?
“Yanzu misali mu na hulɗa da masu saida magunguna, sai a ce me ya haɗa Hukumar Tace Finafinai da magani? Mu ba ‘content’ ɗin maganin ne matsalar mu ba, a’a, lafazin da aka yi amfani da shi wurin tallar maganin ko a rubutu ko a maganance da hoton da aka sa don tallar magani idan na tsiraici ne; wannan shi ne matsalar mu da kai.

“Sannan masu hoto, ba tun yanzu su ke da abin ba. Da ma abin ya na nan, kuma yanzu an ɗauki mataki ne na cewa in an ɗauki doka, sai mutane sun ga doka sai su ga cewa kamar yanzu aka yi.
“Ka san ita Kano, Hukumar Tace Finafinan ta irin ta daban ce, saboda haka wani ya na wata jihar sai ya ga jihar su babu irin waɗannan abubuwan. Mu kuma yawan kiyaye addinin mu da al’adar mu ya sa kullum ake yin waɗannan abubuwan, saboda tsaftace abubuwan, kada a bar su kara-zube, har abubuwa su zo su lalace.
“Yanzu bari in faɗa maka wani abu. Akwai ‘petition’ da aka kawo mana a kan wani ya je ya yi hoto da iyalin sa, kawai mai situdiyon ya ɗauka ya yaɗa a yanar gizo.
“Ka ga wannan wani abu ne da ka yi don kan ka, amma shi ya je ya ɗauka ya saka a yanar gizo ba tare da izinin ka ba.
“Don haka dole mu ce ga yadda tsarin nan ya ke, saboda ba ko wane irin hoto za ka rinƙa sa mana ba.

“Saboda haka situdiyoyin nan dole mu rinƙa binciken su, mu san waɗanne irin hotuna da menene ka ke yi da sauran su, kada ya zamto abu ya zama na masha’a, da sauran su.”