• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Al’ummar Barwa sun yaba wa minista Sadiya saboda rijiyar burtsatse da asibiti

by DAGA WAKILIN MU
October 18, 2020
in Nijeriya
0
A wajen taron a ƙauyen Barwa

A wajen taron a ƙauyen Barwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
AL’UMMAR ƙauyen Barwa da ke Yankin Birnin Tarayya (FCT) sun yaba wa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya saboda ta gina masu asibiti da rijiyar burtsatse don samun ruwan sha.
 
Mai’unguwar ƙauyen, Cif Monday Kogi, shi ne ya furta yabon a  lokacin da Minista Sadiya Umar Farouq da wasu jami’an ma’aikatar su ka je Barwa domin ƙaddamar da bikin Ranar Magance Fatara ta Duniya ta shekarar 2020 wanda aka yi a ranar Asabar.
 
Cif Kogi, wanda ya bayyana godiya ga Gwamnatin Tarayya, ya tuno da cewa ƙauyen ba ya da ruwan sha da asibiti har sai da ma’aikatar ta kai masu ziyara a bara.
 
Ya ce: “Tun zuwan ku na farko a ranar 17 ga Oktoba, 2019, mun ga yadda aka gina mana rijiyar burtsatse da asibiti a ƙauyen Barwa. A madadin jama’ar Barwa, mu na maku godiya.”
 
Shugaban al’ummar ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta katange asibitin kuma ta gina hanyar zuwa ƙauyen daga filin jirgin sama.
 
A jawabin ta, Hajiya Sadiya Umar Farouq, wadda Daraktan Harkokin Agaji, Mista Ali Grema ya wakilta, ta ce ta yi murna da ƙaddamar da bikin Ranar Magance Fatara ta Duniya a wannan ƙauyen. 
 
Ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki da hukumomin da ke ƙarƙashin ta don tabbatar da an cimma burin Shugaban Ƙasa na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga fatara a cikin shekara 10.  
 
Ta ce, “Wannan rana ta musamman ta bada dama a fahimci irin ƙoƙari da faman da mutane masu fatara ke yi da kuma damar su faɗi abin da ke damun su.
 
“An shafe shekaru ana yaƙi da fatara a yayin da kashi arba’in cikin ɗari na al’ummar Nijeriya su na rayuwa ne cikin ƙunci kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta bayyana. Ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnati shi ne a taimaka wa dukkan jama’a kuma a ba su kariyar da ta dace domin yaƙi da fatara abu ne da ke cikin ran gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. 
 
“Wannan gwamnatin ta kasance mai sadaukarwa ga manufofi da tsare-tsaren kula da mutane masu ƙaramin ƙarfi na duniya kuma za ta yi aiki da manufofin ƙasa da ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya.”
 
Ita dai Ma’aikatar Harkokin Agaji, ta zaɓi ƙauyen Barwa ne a matsayin inda za ta fara wannan bikin na Ranar Magance Fatara ta Duniya a bara tare da taimaka wa ƙauyen ta hanyar gina masu wurin shan magani da kuma sama masu wurin ɗibar ruwan sha ta hanyar shirin taimakon al’umma, wato ‘Community and Social Development Project’ (CSDP).
 
A bana, ma’aikatar ta bada kyautar wuraren wanke hannu guda uku da kayan wanki da su ka haɗa da sabulai, ƙyallayen rufe fuska da magungunan tsaftace hannu ga iyalai, da kuma tukunyar jama’a  saboda wannan ranar, a yayin da ministar da sauran jami’ai su ka yi wankin hannayen su na gwaji ga jama’a.
 
Jigon bikin na bana dai shi ne “Aiki Tare don Cimna Adalcin Al’umma da Yanayi ga Kowa”, wato ‘Acting Together to Achieve Social and Environmental Justice for All”.

Loading

Previous Post

Cewar Hamisu Breaker: Ba da ni za a yi shari’a ba

Next Post

Ministar Agaji ta ƙaddamar da shirin bada lamuni ga mata a Filato

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Hajiya Sadiya Umar Farouq da Madam Pauline Tallen wajen miƙa buhunan abincin agaji daga Rumbun Abinci na Ƙasa, a Jos

Ministar Agaji ta ƙaddamar da shirin bada lamuni ga mata a Filato

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!