ALHAMDU lillah! Cikin yardar Allah an ɗaura auren Editan jaridar Rariya kuma jarumi a Kannywood, Aliyu Ahmad.
Kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito maganar kwanan nan, hakan kuwa aka yi; an ɗaura auren na Aliyu da sahibar sa Hauwa Sa’idu Gambo a jiya Juma’a, 12 ga Fabrairu, 2021 a masallacin Juma’a na Babbar Kasuwar Muhammadu Buhari da ke garin Karu, yankin Abuja, da misalin ƙarfe 2 na rana bayan an kammala sallar Juma’a.
An ɗaura auren a bisa sadaki N100,000.
Ɗimbin jama’a tare da manyan ‘yan jarida da su ka fito daga jihohin Nijeriya sun halarci taron ɗaurin auren. Daga cikin su akwai mai ba shugaban ƙasa shawara a kan soshiyal midiya, Bashir Ahmad, Sani Musa Maira, Bashir Babandi Gumel, Umar El-Farouk, Sa’eed Nagudu, Abbas Sadiq da Isah Abubakar Kare.

Da yammacin ranar kuma, an shirya ƙasatacciyar dina a wani ɗakin taro mai suna Global Suite da ke Titin Abuja zuwa Nassarawa.
An fara taron dinar da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, har zuwa ƙarfe 10:00 na dare.
Jarumi kuma mawaƙi Abbas Sadiq da mawaƙi Sa’eed Nagudu sun nishaɗantar da taron.
Kafin ranar ɗaurin auren dai, wato a ranar Laraba, 10 ga Fabrairu, an yi bikin Ranar Fulani, sai kuma ranar Alhamis aka yi kamu.
Mu na addu’ar Allah ya ba sababbin ma’auratan zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

