• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ambaliya da ke tafe: Minista ta gargaɗi jihohi da ƙananan hukumomi kan aikin kwashe jama’a

by DAGA WAKILIN MU
October 18, 2022
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq a wajen taro da 'yan jarida

Hajiya Sadiya Umar Farouq a wajen taro da 'yan jarida

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta faɗakar da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi da ma shugabannin jama’a, musamman a jihohin Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa, cewa ambaliyar ruwa na nan tafe a cikin makwanni masu zuwa, sannan ta yi kira a gare su da su shirya wa aikin kwashe jama’ar da ke zaune a yankuna da hanyoyin da ruwan ke bi. 

Ministar ta faɗi haka ne a taron da ta yi da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja domin bayyana masu ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage raɗaɗin bala’in ambaliya a ƙasar nan, wanda ta ce babbar matsala ce.

Hajiya Sadiya ta ce duk da gagarumin ƙoƙarin da ake yi na kauce wa matsalolin ambaliyar wannan shekarar ta 2022 kamar yadda Hukumar Nazarin Yanayi ta Nijeriya ta hango zai faru, gwamnatocin jihohi da dama ba su yi wani shiri dangane da ambaliyar ba, wanda hakan ya jawo babbar asarar rayuka da ɓarnata dukiyoyi.

Ta ce: “Abin baƙin ciki ne a ce an rasa rayuka sama da 603 ya zuwa yau 16 ga Oktoba, 2022. Jimillar mutum 1,302,589 su ka gudu daga muhallin su, mutum 2,504.095 abin ya shafa baki ɗaya, mutum 2,407 sun ji rauni, jimillar gidaje 82,053 sun rushe baki ɗaya, yayin da guda 121,318 su ka lalace a wasu sassa nasu. Hekta 108,392 ta gonaki ta lalace a wasu sassa yayin da hekta 332,327 ta salwanta baki ɗaya, wanda ya haɗa da hanyoyi da yawa da sauran muhimman ababen more rayuwa.

“A yayin da mu ke alhinin haɗarin nan mai ban takaici na kifewar kwale-kwale da ya faru a Jihar Anambara da sauran wurare, don Allah mu lura da cewa ba wai gaba ɗaya ba mu san abin da ke faruwa ba ne domin kuwa Hukumomin Nazarin Yanayi su na ta gargaɗin cewa jihohi irin su Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa su na fuskantar barazanar faɗawa bala’in ambaliya har zuwa ƙarshen Nuwamba.

“Mu na kira ga gwamnatocin waɗannan jihohin da ƙananan hukumomi da al’ummomi da su shirya wa kwashe mutanen da ke zaune a wuraren da ambaliya ke bi zuwa wurare masu tudu, su samar da tantuna da kayan agaji, da ruwan sha da kuma kayan magani saboda yiwuwar ɓarkewar annobar cututtuka.” 

Bayan haka, wata babbar tawaga da ma’aikatar ta kafa ya na nan ya na shirin kai wa gwamnonin jihohi ziyara domin ganawa da su kan su ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa shirin su na tunkarar matsalar ambaliyar kamar dai yadda aka tsara a Shirin Gaggawa kan Ambaliya na Ƙasa, wato ‘National Flood Emergency Preparedness and Response Plan’. 

Ana sa ran masu ruwa da tsaki a lamarin za su yi aikin da aka rataya masu a wuyan su domin hana aukuwar mace-mace saboda ambaliya ko wasu cututtuka da ke da alaƙa da rashin lafiya daga al’amarin wanda ka iya faruwa.

Bugu da ƙari, Babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, zai jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Kamaru a watan gobe domin su tattauna da hukumomin ƙasar kan batun buɗe dam ɗin Lagdo jefi-jefi. 

Haka kuma kwanan nan za a aiwatar da Shirin Gaggawa kan Ambaliya na Ƙasa domin a samu daidaito wajen aikin tunkarar matsalar ambaliya, sannan a samar da hanyar gudanar da aikin kula da ambaliya a matakan ƙasa baki ɗaya daga sama har zuwa ƙasa.

Minista Sadiya tare da manema labarai da shugabannin ma’aikatar ta

Bayan haka, kusan dukkan jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya sun karɓi kayan abinci da waɗanda ba na abinci ba domin rage matsaloli daban-daban na bala’in ambaliyar.

Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Alhaji Mustapha Habib Ahmed, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da ministar ta yi da manema labarai. 

Ya ce: “Labarin da wasu ke yaɗawa cewa wai ba a ga abin da Gwamnatin Tarayya ta yi a jihohin da ambaliya ta shafa ba ƙarya ne. Mu na nan a kowace jiha ta ƙasar nan. Mun kai kayan agaji a kowace jiha ta ƙasar nan. 

“Kuma mu na gode wa Babban Kwamandan Askarawa kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da mai girma Minista. 

“Za mu ci gaba da yin ƙoƙarin mu wajen sama wa ƙasar nan agaji.”

Waɗanda su ka halarci taron dai sun haɗa da Babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, da shugabannin hukumomi da daraktocin ma’aikatar.

Loading

Tags: ambaliyar ruwaharkokin agajikayan agajin gaggawakwashe mutaneMuhammadu BuhariMustapha Habib AhmedNasir Sani GwarzoNEMASadiya Umar Farouq
Previous Post

Furodusar Kannywood, Fatima Lamaj ta taya Yusuf Costume murnar auren sa da Maryam

Next Post

Ina samun alheri tun da na rikiɗe daga jaruma zuwa mawaƙiya – Zakiyya Ibrahim

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Zakiyya Ibrahim

Ina samun alheri tun da na rikiɗe daga jaruma zuwa mawaƙiya - Zakiyya Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!