AN ɗaura auren jarumin barkwanci Ayatullahi Tage da amaryar sa Hauwa Muhammad Isah (Hauwa Madu) a safiyar ranar Lahadi, 17 ga Nuwamba, 2024.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 11 a unguwar Tudun Murtala Kwanar Tifa a Kano ya samu halartar jama’a da dama da suka zo domin su shaida.
‘Yan fim da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da fitaccen jarumi Nuhu Abdullahi.


