A JIYA Asabar, 27 ga Mayu, 2023 aka ɗaura auren sanannen mai ba da sutura kuma jarumi a Kannywood, Sadiqu Ahmad (Artiste).
An ɗaura auren sa da abar ƙaunar sa, Amina Aminu (Hajiya), da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Wudilawa da ke Titin Gidan Sarki, kusa da sakatariyar Municipal, a Birnin Kano, a bisa sadaki N100,000.
Ana kammala ɗaura auren sai angon ya yi sujjada ya yi wa Allah godiya.

Ɗaurin auren ya samu halartar ‘yan Kannywood da dama da su ka haɗa da Hafizu Bello, Alhassan Kwalle, Abdul Amart, Sadiq Mafia, Mansoor Sadiq, Nura Manaja, Tahir I. Tahir, Wassh Waziri Hong, Mu’azzam Idi Yari, Alin D-Man, da sauran su.
Kafin ranar ɗaurin auren, an yi ƙasaitaccen dina, wanda shi ma ‘yan Kannywood da dama sun halarta.

Ango ya yi godiya ga Allah da kuma sauran jama’a da su ka halarci bikin sa, inda ya ce, “Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa, mai komai. Saƙon godiya ga dukkanin mutanen da su ka samu damar halartar zuwa wajen shagalin aure na da kuma waɗanda ba su samu damar zuwa ba su ka yi min addu’a, na ji daɗi sosai.
“Allah ya saka wa kowa da alkhairi. Na nesa kuma Allah ya mai da kowa gidan sa lafiya. Na gode.”

