FITACCEN mawaƙin nan da ke Kaduna, Malam Yahaya Makaho, ya ƙaddamar da wata gidauniya mai suna ‘Malam Yahaya Makaho Foundation’, wadda zai riƙa amfani da ita wajen taimaka wa naƙasassu ‘yan’uwan sa.
An ƙaddamar da gidauniyar a wani taro da aka yi a Ado Kachia Plaza da ke Titin Constitution, cikin garin Kaduna, a ranar Asabar, 1 ga Fabrairu, 2020.
Da ya ke jawabi a wurin taron, fitaccen malami mai wa’azi, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya ce, “Mun zo mu taya ɗan’uwan mu Malam Yahaya Makaho murnar ƙaddamar da wannan gidauniya.”
Malamin ya janyo ayoyi daga cikin Alƙur’ani mai girma da su ka yi nuni da muhimmancin irin wannan taro.

Ya ci gaba da cewa, “Ina jinjina wa Malam Yahaya Makaho da wannan abu da ya yi, domin ya tanadarwa kan sa sadaka mai gudana.
“Mu na fatan Allah ya sa ya zama sadaƙatuj jariya a gare shi.
“Malam Yahaya mu na yi maka addu’a, Allah ya saka maka da alheri.”
Sheikh ya yi jan hankali ga gwamnati, inda ya ce, “Ya kamata a ce gwamnati ce za ta rinƙa irin wannan, amma ba za su yi ba.
“Yanzu in da wata sharholiya ce, da yanzu an cika wurin nan da manyan mutane.
“Mu na kira ga gwamnatin ƙasar nan da su yi ƙoƙari su duba wannan al’amari.”
A ƙarshe ya rufe jawabin nasa da hadisin da ke nuni da abubuwan da ke haddasa bala’i a ƙasa.
Daga nan sai mai gabatarwa, Malam Abubakar Yusuf Ladan, ya tada uban gayyar, wato Malam Yahaya Makaho ya gabatar da nasa jawabin.
Malam Yahaya ya faɗi abubuwan da su ka ba shi ƙwarin gwiwar kafa ‘Malam Yahaya Makaho Foundation’.

Ya ce jikin, “Sanin kowa mu a nan Arewa mutanen da su ka samu naƙasa ko masu buƙata na musamman, kamar yadda mu ka ƙirƙirar wa kan mu don daraja kan mu, maimakon a kira ka gurgu ko makaho, sai mu dunƙule shi wuri ɗaya mu ka maida shi masu buƙata na musamman.
“A lokacin da na shigo garin Kaduna na jaraba abubuwa daban-daban don ganin na kare mutuncin kai na. Ban kuma gane abin da na ke yi ya na da muhimmanci ba sai da na shiga fagen waƙa, na kuma jure wa faɗi-tashi da ya kamata a ce sun dakatar da ni, amma kuma na kasa dakatawa saboda tunani da miƙa komai ga Ubangiji.
“A baya, na halarci tarukan makafi da guragu, a ce wata barista ce ko kuma wani babban mutum ne ya tara mutane don a samar mana mafita.
“Da farko na ɗauka da gaske mu ake nema wa mafita, sai daga baya na gane cewa su su ke nema wa kan su mafita.
“Idan aka yi duba, mu ‘yan Arewa an ɗauka dukkan mu Musulmai ne, amma Musuluncin mu bai hana irin wannan ɗabi’u na ci da haƙƙin mutane ko kuma in ce ci da ceto kamar yadda wasu mutane su ke kiran shi ba.

“Wasu Malam su na ƙoƙarin nuna kula da haƙƙin naƙasassu. Wasu kuma tunanin hakan ya yi ƙaranci a tattare da su.
“Yau idan ka je Jihar Legas, duk inda za ka ga depot ɗin almajirai, babu kowa a ciki sai ‘yan Arewa, kuma daga Arewa su ke tashi su tafi Legas su yi bara.
“Haka idan ka je Inugu ko Onicha, duk inda za ka ga almajirai za ka tadda ‘yan Arewa ne.
“Kuma da Allah ya tashi halitta babu wani ɓangare da bai yi masu mutane masu naƙasa ba.
“Wannan abin da na zauna sai na yi tunani tare da shawarar Ɗan’amanar Dutse Alhaji Nasiru Dano, da taimakon Allah da taimakon wasu mawaƙa, ya na san Alhaji Nasiru Dano, kuma ya ba ni dukkan wata gudunmawa da ya kamata, wanda ya kawo matakin da na ke taƙama ko alfahari da ita a yanzu.
“Ya ce mani, ‘Malam Yahaya, za mu taimake ka, kai ma ka taimaki ‘yan’uwan ka masu buƙatar tallafin nan’.

“Wannan dalili ne ya sa ni ni kuma na ɗauki maganar sa da muhimmanci. Da ma kuma ina da kyakkyawan tunani, musamman ganin cewa ina da lalura irin na ‘yan’uwa na, sai na ga cewa duk abin da zan yi na faɗakarwa ta dalilin waƙa, zan duba in ga idan ya ɗauki hanyar da ko bayan babu ni za a iya kwatance da ni, a ce an taɓa yin wani mutum da ba ya gani, ya ƙirƙiri ‘foundation’ don taimaka wa ‘yan’uwa naƙasassu.”
A ƙarshe ya ce, “Ina mai bada shawara, musamman ga shugabannin da su ke da kyakkyawar tunani a kan naƙasassu, da su tuna cewar dukkan su nauyi ne a wuyan su.
“Kuma mutuntawar da na ke samu daga mutanen gari zai ƙara ƙaruwa ne in gwamnati ta nuna mu na da mutunci. A taƙaice, wannan shi ne dalilin da ya sa na ƙirƙiri ‘foundation’ don in taimaka wa ‘yan’uwa na mabuƙata.”
Haka dai sauran manyan baƙin da su ka halarci taron su ka yi jawabai masu ratsa zukata.
Daga cikin su akwai Hakimin Kakuri, Alhaji Shehu Tijjani, wanda shi ne uban taro, da Honarabul Hassan Muhammad, tsohon kwamishinan kuɗi na Jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Goron Namaye, Alhaji El-Sa’id Yakubu Lere, Injiniya Uba Dauda, Malam Sa’idu Gombe da fitacciyar jaruma Hajiya Hadiza Aliyu Gabon.
Bayan gabatar da jawabai kuma sai aka shiga abin da ya tara mutane a wurin, wato raba kekunan guragu.
Wata ƙungiya mai suna ‘Blaky Needy Initative’, ita ma ta raba barguna da rigunan sanyi ga dukkan waɗanda aka raba wa kekuna.
Aƙalla an raba kekuna sama da sittin a wurin taron.
An fara taron da misalin ƙarfe 10:40 na safe, aka tashi da misalin ƙarfe 1:30 na yamma.

Wasu daga cikin mawaƙa da ‘yan fim da su ka halarci taron sun haɗa da Aminu Ala, Yakubu Lere, El-Mu’az Birniwa, Hadiza Gabon, Sadiya Yarima, Hannatu Bashir, Umar Ɗan Hausa, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Ahmad Yariman Tiga, Yusuf Jumare, Abubakar Mai Bibbiyu, Anas M. Shadda, da sauran su.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin kafa gidauniyar ta Malam Yahaya Makaho a ranar Asabar, 25 ga Janairu, 2020.