MASU shirya Biki Da Baje-kolin Finafinan Harsunan Gadon Afrika na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF Awards), sun bayyana cewa sun kai matakin tantance finafinan da su ka shiga gasar domin fitar da waɗanda za su kai matakin cancanta.
Alƙalan gasar, wadda aka saba shiryawa a duk shekara, su bakwai ne: Victor Okhoir, Emmanuel Emascalu, Charlas Okwuowulu, Falakemi Ogungbe, Izu Ojukwu, Charity Torut, da Alwine Allen.
Mujallar Fim ta gano cewa a bana an samu ƙarin finafinai da su ka shiga gasar fiye da shekarun da su ka gabata, inda aka samu guda 46 daga ƙasashe da su ka haɗa da Nijeriya, Masar, Afrika ta Kudu, Tunisiya, Ghana, Tanzaniya, Aljeriya, Ajantina, Benin, Botswana, Kamaru, Kodebuwa, Jamus, Gini Bissau, Kenya, Malawi, Mozambik, Potugal, Amerika da kuma Zumbabuwe.
Haka kuma Daraktan Gudanarwa na KILAF Awards 2023, Alhaji Nasir B. Muhammad, ya yi wa mujallar Fim ƙarin bayanin cewa, “A wannan shekarar an samu sauye-sauye. Saboda cigaban zamani da ake samu, don haka tantancewar ma ta onlayin ake gudanar da ita, saboda alƙalan sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya, don haka sai aka tsara gudanar da tantance su ta onlayin. Amma a mataki na ƙarshe za a haɗu a waje guda don fita da sakamakon gasar.”
Ana gudanar da gasar KILAF ne da iya zallar yaren mutanen Afrika, don haka duk wani fim da za a shigar dole ne ya zama yaren da aka yi fim ɗin ya zama ɗaya daga cikin harsunan nahiyar ko a wace ƙasa aka yi shi.
Sannan lallai ne fim ɗin ya zama na ‘yan makaranta ko na tarihi, ko gajeren fim, ko kuma wanda ya shafi rayuwar yau da kullum.
A watan gobe ake sa ran za a gudanar da babban taron baje-kolin a Kano. Manyan baƙi daga ƙasashe za su halarta.
Za a yi taron daga ranar 21 zuwa 26 ga Nuwamba, 2023.