WANI kwamiti da fitaccen ɗan jarida Jaafar Jaafar ya kafa ya yi kasafin zunzurutun kuɗi har naira miliyan biyar domin inganta rayuwar shahararriyar zabiyar nan Magajiya Ɗambatta.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda Jaafar ya gano zabiyar a garin Makoɗa cikin Jihar Kano, ta na rayuwa cikin ƙunci, har da bara domin samun abinci.
Jaafar da wasu aminan sa sun kafa gidauniya don tara kuɗin da za su yi amfani da su wajen ceto rayuwar zabiyar mai waƙar ‘Soriyal’ daga halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Ya zuwa lokacin da mu ka ba labarin a makon jiya, jama’ar Annabi da su ka ga bayanan Jaafar sun tara kuɗin agaji sama da N400,000.
To ya zuwa jiya kuma kuɗin sun kai har naira miliyan biyar da dubu shida da ɗari biyu da ashirin da biyu (N5,006,222).
Jaafar ya bayyana cewa mutane 576 ne su ka bada gudunmawar wannan kuɗin.
Mujallar Fim ta ga cewa a jerin sunayen waɗanda su ka bada gudunmawar akwai wanda ya bada har rabin miliyan, to akwai kuma wanda ya bada N200 kacal.

Jaafar ya ce a yanzu dai an rufe karɓar taimakon, ya na mai farin ciki da cewa abin da aka tara ya zarce tunanin ‘yan kwamitin nasu.
Haka kuma ya bayyana cewa sun ziyarci Magajiya Ɗambatta a Makoɗa jiya, inda shi da sauran ‘yan kwamitin (Musa Sufi, Ibrahim Sanyi-Sanyi, da Munzali Hausawa) su ka labarta mata abin da aka tara da kuma nufin su game da wannan kuɗi.
Magajiya ta yi godiya ga duk wanda ya taimaka ya bada wannan agaji gare ta.
Wani likita, Dakta Kabir Abdussalam, ya binciki lafiyar mawaƙiyar, kuma ya bada shawarar cewa za a kai ta asibiti a sake duba lafiyar idon ta, da fatan ko za a yi dace a magance mata makantar da ta yi.
Jaafar ya ce sun jima a garin su na bincike tare da tattaunawa da ‘yan’uwan ta da maƙwabtan ta da dattijan garin kan abin da ya dace a yi.
‘Yan kwamitin sun sa wani dillali a garin ya nemo filin sayarwa inda za a gina mata gida ko kuma idan an samu gidan sayarwar ma ana so.
An ware kuɗi masu dama domin a gina mata gida ko kuma a sayi ginanne.
Jaafar ya sanar da cewa an kasafta kuɗi domin kula da Hajiya Magajiya Ɗambatta a tsawon shekara uku masu zuwa.
Kasafin, wanda mujallar Fim ta gani, shi ne:
1. Kuɗin kashewa a duk wata: N15,000. Za a riƙa ba ta N5,000 a kowane kwana 10. Kuma ita za a ba kuɗin kai-tsaye. Jimilla a shekara ɗaya shi ne N180,000.
2. A duk bayan wata huɗu za a ba ta N15,000 kuɗin sayen sabulu, man shafawa, turare da sauran su. N5,000 za a riƙa ba ta a duk wata. Jimilla a shekara ɗaya shi ne N60,000.
3. Za a ba ta N40,000 kuɗin kayan Sallah a duk shekara, wato N20,000 a kowane bikin Sallah kenan.
4. N12,000 kuɗin abincin rana da na dare a kowane wata. N200 sau 2, wanda ya kama N400 sau kwana talatin. Za a bada waɗannan kuɗi ga wasu jikokin ta biyu maza masu aure waɗanda su za su riƙa ciyar da ita. An shawarta cewa idan wannan jika ya ciyar da ita tsawon wata ɗaya, sai ɗayan ya amsa, shi ma wata ɗaya. An yi haka ne don a samu sauƙi da tabbatar da komai ya tafi daidai. Jimillar wannan kuɗi a shekara shi ne N144,000.
5. Za a riƙa ba wata jikanyar ta alawus ɗin N5,000 a duk wata domin kula da tsaftar ta. Wannan yarinya ita ce mai share mata ɗaki kuma ta wanke mata sutura. Jimilla a shekara shi ne N60,000.
6. Za a ba yarinyar nan ‘yar jagorar Magajiya N3,000 na zuwa makaranta a duk wata. Wato ya kama N100 a kowace rana, sau kwana 30. Za a damƙa kuɗin a hannun uwar ita ‘yar jagorar. Jimilla a shekara shi ne N36,000.

Jimillar dukkan waɗannan kuɗaɗe a shekara ɗaya shi ne N520,000.
Jimillar waɗannan kuɗaɗe da za a kashe a shekara 3 shi ne N1,560,000.

Mujallar Fim ta fahimci cewa da yake jimillar kuɗin sun kai miliyan biyar, za a cire waɗannan miliyan ɗaya da rabi da ‘yan kai, sannan a cire kuɗin sayen gida ko gina gida daga ciki (bakin abin da ya kama), daga nan kuma abin da ya rage za a aje shi saboda gaba.
Jaafar ya bayyana cewa ko ƙwandala kwamitin su ya kashe kan wannan hidima, to zai yi bayani a kan ta, duk duniya ta gani.

A kafafen soshiyal midiya dai ana ci gaba da yi wa su Jaafar ruwan yabo da addu’ar Allah ya biya su ladar wannan namijin ƙoƙari da su ka yi na ceto rayuwar Magajiya Ɗambatta daga halin ƙunci da ta shiga.