AN gurfanar da shahararren mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Rijiyar Zaki a Kano kan kuɗi naira miliyan goma da dubu ɗari uku (N10.3m).
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa wani mutum mai suna Muhammad Ma’aji ne ya yi ƙarar mawaƙin kan waɗannan kuɗaɗe da ya ke bin sa.
Ma’aji ya shaida wa kotu cewa akwai wata harka su ka ƙulla shi da Rarara a watannin baya, amma yanzu ba shi da wani zaɓi don ya karɓi haƙƙin sa sai ta fannin shari’a.
Ya ce ya bi matakin sulhu da Rarara don ya ba shi kuɗin sa tunda dai harkar da su ka kulla ba ta yiwu ba, amma mawaƙin ya ƙi biyan shi.
Kakakin manyan kotunan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano, Malam Muzammil Ado Fagge, ya bayyana yadda Rarara ya dinga wasan ɓoyo da masinjan kotu don kada a ba shi sammaci.
Ya ce: “Wannan ƙara ce wadda Muhammad Ma’aji ya shigar da Rarara, kuma ƙara ce wadda akwai mu’amulla da shi har ta naira miliyan 10 kuma ya yi ya yi ya bashi ƙuɗin amma ya ƙi.
“Don haka mun yi amfani da doka da oda ta 9, 2021 da ta yi magana cewa idan aka nemi mutum don a ba shi sammaci ba a gan shi ba to za a iya yin amfani da shafukan sada zumunta don sanar da shi ko kuma a liƙa masa a gidan sa.
“Shi wannan mawaƙin sai wasan ɓuya ya ke yi da jami’in mu don ya ba shi sammacin amma ya ƙi yarda su haɗu, shi ya sa mu ka nemi mai unguwar sa da kuma shaidu mu ka liƙa masa a gidan sa da ke Zoo Road, domin tabbatar da bin doka wajen isar masa da saƙon kotun.”
Malam Muzammil ya ce za a fara sauraren ƙarar a ranar Talata mai zuwa, 11 ga Afrilu, 2023 a kotun wadda Mai Shari’a Halhaltul Khuza’i Zakariya ke jagoranta.