
A SAFIYAR yau ɗimbin ‘yan fim da jama’ar gari da ‘yan’uwa su ka halarci jana’izar marigayi darakta a Kannywood, Aminu S. Bono, wanda Allah ya yi wa rasuwa jiya a Kano.
An yi wa mamacin sallah a gidan su da ke unguwar Ɗandago, inda daga nan aka ɗauke shi aka ɗunguma zuwa maƙabartar Ɗandolo da ke unguwar Goron Dutse, aka rufe shi a can.
Daga nan aka koma gidan su marigayin domin ci gaba da karɓa gaisuwa daga masu zuwa ta’aziyya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Aminu S. Bono, wanda kuma jarumi ne a masana’antar finafinan, ya rasu ba zato ba tsammani jiya da yamma a sanadiyyar ciwon ciki.
Rasuwar sa ta girgiza ‘yan fim da iyalan sa matuƙa, musamman ganin cewa ya tashi lafiya ƙalau har ya shiga gari wajen ayyukan sa.
Kowa ka gani a wajen jana’izar kamar ruwa ya ciwo shi saboda damuwa da kuma baƙin cikin rasa ran Aminu. Ana ta jajanta wa juna.
A nan, ga hotunan jana’izar da kuma zaman ta’aziyya da mu ka samu daga shafin Facebook na Ahmad Nagudu.





