BABBAN Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi, ya bayyana cewa kiran da wasu ke yi wa ogan nasa, Farfesa Mahmood Yakubu, na ya fito ya shiga takarar shugaban ƙasa duk shirme ne.
A cikin ‘yan kwanakin nan akwai masu faɗin cewa wai kada ‘yan Nijeriya su yi mamaki idan su ka ji shi ma Farfesa Yakubu ya shiga da’irar masu neman zama shugaban ƙasar nan a manyan zaɓuɓɓukan da za a yi a 2023.
A lokacin da ya ke martani kan wannan maganar, Oyekanmi ya ce, “Ba za ta taɓa saɓuwa ba – wai bindiga a ruwa.”
Ya nanata cewa ogan sa zai ci gaba da kasancewa “alƙalin da ya maida hankalin sa kacokam ga tabbatar da an yi zaɓe fisabilillahi kuma mai nagarta.”
A takardar sanarwar da ya rubuta, sakataren yaɗa labaran ya ce: “An ja hankalin mu ga shaguɓen da wasu ke yi cewa wai kada ‘yan Nijeriya su yi mamaki idan sun ji shugaban INEC ya shiga takarar shugaban ƙasa ko su na kiran sa da ya shiga ɗin. Wannan gurguwar shawara ce. Ba za ta taɓa saɓuwa ba.
“Shugaban zai ci gaba da kasancewa alƙalin da ya maida hankalin sa kacokam ga tabbatar da an yi zaɓe fisabilillahi kuma mai nagarta.
“Haƙƙin da tsarin mulki ya ɗora masa a matsayin Babban Kwamishinan Zaɓe na Tarayya kuma Malamin Zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa muƙamai ne masu daraja da su ka ishe shi da har za a ce ya yi tunanin kaucewa zuwa wani al’amari da ya saɓa wa doka, sanin ya-kamata da kuma aƙidun karan kan sa.
“Shugaban zai ci gaba da sauke nauyin da ke kan shi ba tare da nuna so ko ƙi ga wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara ba.”