SHUGABAN Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Dakta Ahmad Sarari, da tsohon shugaban ƙungiyar, Alhaji Sani Mu’azu, sun samu shiga cikin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar nan mai kare haƙƙin masu basirar ƙirƙira ta Nijeriya, wato ‘Audio Visual Rights Society’ (AVRS).
An zaɓe su ne tare da shugaban ƙungiyar, Mahmood Alli-Balogun, wanda ya ƙara cin zaɓe a karo na biyu.
A labarin da mujallar Fim ta samu, an bayyana cewa an zaɓi Alli-Balogun, Jide Kosoko da Sani Mu’azu ne a matsayin daraktocin ƙungiyar ba tare da hamayya ba a taron ƙungiyar na shekara-shekara, karo na 5, wanda aka yi a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2021 a Airport Hotel da ke Ikeja, a Legas.

Sai dai a ɓangarorin furodusoshi, ‘yan wasa da marubutan labarin fim an yi zaɓuɓɓuka ne inda aka cike guraben da ke akwai a kwamitin gudanarwar.
A nan ne aka zaɓi Dakta Sarari, Cif Peddie Okao da Dattijo Tunji Ojetola a ɓangaren marubutan labarin fim (screenwriters), a yayin da kuma aka zaɓi Aina Kushoro (Kush), Nobert Ajaegbu da Iyen Obaseki-Omoruyi a matsayin furodusoshi.
Haka kuma an zaɓi Monalisa Chinda, Ejike Asiegbu da Yemi Solade a matsayin jagororin ‘yan wasa.
Manyan manishaɗanta da su ka halarci taron sun haɗa da Alex Eyengho, Madu Chikwendu, Lilian Amah-Aluko, Tony Anih, Zeb Ejiro, Sonny MacDon, Olorogun Fred Amata da wasu da dama.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ita dai ƙungiyar AVRS ita kaɗai ce ƙungiyar da aka yarda da ita ta wakilci masu shirya finafinai da mawaƙa wajen ƙwato haƙƙin su a hukumance.
An kafa ƙungiyar ne a unguwar Surulere, a Legas a ranar 11 ga Yuli, 2013.
Ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ta sanya a gaba shi ne yaƙi da masu satar basira da yadda za a gyara dokar haƙƙin mallaka don ta yi daidai da muradin manishaɗanta, wato masu harkar nishaɗi kamar ‘yan fim da mawaƙa.
Mahmood Alli-Balogun, wanda aka sake zaɓa jiya, shi ne shugaban ta na farko.