• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ana neman ɓata mana suna kan shugabancin APGA, inji INEC

by DAGA WAKILIN MU
May 11, 2023
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa surutan da wasu ke yi kan cewa ta ƙi bin umarnin kotu dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar APGA wani yunƙuri ne na ɓata mata suna.

Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Zaɓe na hukumar, Lauya Festus Okoye, ya faɗi a wata sanarwa ga manema labarai cewa hukumar ta lura da yadda wata ƙungiya da ba a gane kan ta ba ta ke yamaɗiɗi kan al’amarin, ta na rarraba fastoci da yin surutai inda ta ke zargin hukumar da ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli da ya ce wai wani mai suna Cif Edozie Njoku ne “Shugaban APGA na Ƙasa na gaskiya”.

Hukumar ta ce ana yaɗa waɗannan fastocin da surutan ne don kawai a yi wa INEC sharri da nufin a yaudari waɗanda ba su san gaskiyar abin da ke faruwa ba. 

Okoye ya ce: “Mu na so mu bayyana cewa waɗannan al’amurra fa sun shafi faɗin gaskiya ne tare da bin doka da oda ba wai kwakwazo da neman tada zaune tsaye ba.

“A lura da cewa ƙarar da aka kai kotu ta samo asali ne daga Babbar Kotun Jihar Jigawa, wadda wani mai suna Alhaji Rabi’u Garba Aliyu ya kai a kan Cif Jude Okeke da wasu mutum uku. Cif Edozie Njoku ba ya cikin waɗanda ake ƙara. 

“Ɗaya daga cikin buƙatun da aka nema a wajen kotu shi ne ‘A bayyana cewa shugabannin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance na ƙasa, ciki har da mai ƙarar, waɗanda aka zaɓo su a babban taron ta na ƙasa da aka yi a Owerri, Jihar Imo, a ranar 31 ga Mayu 2019, su ci gaba da riƙe muƙaman su tare da yin ayyukan su har tsawon wa’adin shekara huɗu da za a lissafa daga ranar 31 ga Mayu 2021’.  

“A ranar 30 ga Yuni 2021, Babbar Kotun Jihar Jigawa, a ƙara mai Lamba JDU/022/2021 ta yanke hukunci inda ta ba wannan Alhaji Rabi’u Garba Aliyu nasara. Da aka ɗaukaka ƙarar, sai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa ƙarar da aka kai ba a bi dokar yin shari’a ba. Don haka, dukkan shari’ar da aka yi a Babbar Kotun Jihar Jigawa a ƙara mai Lamba JDU/022/2021, wadda Musa Ubale J ya yanke a ranar 30 ga Yuni 2021 da hukuncin da aka yanke mata duk an hamɓarar da su.” 

Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke a ranar 14 ga Oktoba 2021, ta tabbatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta zartar. 

“Sai dai kuma, a ranar 27 ga Janairu 2023, Cif Edozie Njoku, wanda bai taɓa zama cikin dukkan waɗancan shari’u da aka yi a kotuna daban-daban ba, ya je Kotun Ƙoli ta Nijeriya a matsayin wani wanda ke da ta cewa, ya shigar da buƙatar kotun ta yi gyara a ‘kuskuren rubutu da tuntuɓen alƙalami’ a ainihin babban hukuncin da Kotun Ƙolin ta zartar. An amince masa da hakan, kuma gyaran da aka yi bai shafi gundarin ƙarar da kuma hukuncin da Kotun Ƙolin ta riga ta yanke ba.”

A cewar Okoye, Hukumar Zaɓe hukuma ce mai bin doka da oda kuma za ta ci gaba da bin duk wata doka ko wani hukunci ko umarni da kotuna daban-daban su ka bayar a duk faɗin Nijeriya.

Ya ce, “Ba a ƙin bin umarnin kotunan idan sun ba da umarni ko su ka yanke hukunci ko wata shawara. Kuma su na da ƙarfin hukunta duk wanda ya yi masu tsaurin ido ya ƙi bin umarnin su da hukuncin su a tsarin da su ke da shi. Wannan shi ne abin da duk wani ɗan ƙasa ko wata ƙungiya da ya ke bin doka ya sani, maimakon ya koma ya na neman cin zarafi ko tursasawa ta hanyar wasu ƙungiyoyi marasa alƙibla don kawai a ɓata sunan hukumar da jami’an ta.”

Loading

Tags: APGAEdozie NjokuFestus OkoyeINECJigawamahmood yakubuRabi'u Garba Aliyurikicin shugabanci
Previous Post

Nagari Na Kowa: Tasirin Muhammad Nami A Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji Ta Ƙasa (FIRS)

Next Post

Zaɓen Gwamna: INEC ta kafe sunayen ‘yan takarar zaɓuɓɓukan cike gurbi na jihohin Bayelsa, Imo, da Kogi

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post

Zaɓen Gwamna: INEC ta kafe sunayen 'yan takarar zaɓuɓɓukan cike gurbi na jihohin Bayelsa, Imo, da Kogi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!