MAWAƘAN Hausa biyu da jaruman Kannywood biyu da kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano sun sami muƙamai a cikin ayarin kamfen na ɗan takarar zama shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A jiya Juma’a, 23 ga Satumba, 2022 jam’iyyar ta fitar da jadawalin sunaye da muƙaman waɗanda za su jagoranci kamfen ɗin ta.
Tsarin ya ƙunshi gaggan ‘yan siyasa, ‘yan jarida, mawaƙa da ‘yan fim na Arewa da na Kudu, da sauran su.

A ƙarƙashin jerin mawaƙa da ‘yan fim (performing arts directorate) aka sanya ‘yan Kannywood ɗin, wato mawaƙa Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) da Jadda Garko, da ‘yan wasa Sani Idris Kauru (Moɗa) da Nuhu Abdullahi, da kuma shi Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Isma’ila Muhammad Na-Abba (Afakallahu).
An ba Rarara muƙamin jami’in gudanarwa (admin officer) na Kano, Moɗa kuma dattijo (elder) na Kaduna; Jadda Garko mataimakin darakta (co-deputy director), Nuhu Abdullahi mataimakin jami’in walwala (assitant welfare officer) na Kano, shi kuma Afakallahu shi ne mataimakin darakta (deputy director) na Kano.