AN ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood Fatima Sadisu KK (Fati KK) a yau Juma’a.
An ɗaura auren Fati ne da abin ƙaunar ta Hassan Sani Umar da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan mahaifin ta da ke Titin Mustapha Salihawa, Sabon Kawo, Kaduna.
Kamar dai yadda aka rubuta a katin gayyatar ɗaurin ba a ƙara ko minti ɗaya ba aka ɗaura. Da ma wakilin ango da tawagar sa sun iso wurin ɗaurin auren tun wajen ƙarfe 10:30 na safe.


Bayan an ɗaura auren an yi walima, an ci, an sha, an gyatse.
‘Yan fim da su ka halarci ɗaurin su ne Ibrahim 2-Effects da Ubale 2-Effects.
Amarya Fati KK ta rubuta a Instagram bayan an ɗaura auren cewa, “Finally Mrs Hassan. Alhamdu lillah ya Allah.”
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
