ABIN nan da Hausawa ke kira dakan ɗaka shiƙar ɗaka ya faru a yau lokacin da aka ɗaura auren Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah), da shahararriyar jaruma kuma furodusa, Hajiya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya).
An ɗaura auren su da misalin ƙarfe 2 na rana a yau Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022 a Masallacin Juma’a na unguwar Tishama a Kano a kan sadaki N100,000, wanda aka biya lakadan.
Ɗimbin jama’a na ciki da wajen masana’antar shirya finafinai ta Kannywood sun halarci taron.
Da ya ke gabatar da huɗubar auren, Limamin masallacin, Sheikh Mohammed Jabir, ya hori jama’a da su riƙa kiyaye haƙƙoƙin aure, musamman ma a wannan lokacin da al’umma ta samu kan ta a cikin wani mawuyacin hali.

Haka kuma ya yi kira ga ma’aurata da su riƙa kai zuciya nesa a cikin zamantakewar aure. Daga nan ne sai ya ɗaura auren Isma’il da Ruƙayya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an daɗe ba a ga irin wannan taron ɗaurin auren ba wajen tara jama’a a Kannywood. Wurin ya zama taron sada zumunci da aka daɗe ba a ga juna ba.
‘Yan fim da su ka halarci taron sun haɗa da Adamu Sani, Auwalu Isma’il Marshal, Sani Sule Katsina, Baba Ƙarami, Ado Ahmad Gidan Dabino, Alhassan Kwalle, Alhaji Musa Maikaset, Nura Hussaini, Salisu Officer da sauran su.
Bayan an kammala addu’ar auren, sai mahalarta taron su ka raka ango zuwa gidan su amarya domin gaisuwar surukai.
Abin sha’awa shi ne an yi tafiyar ne a ƙasa daga masallacin zuwa gidan, kuma tafiyar ta ɗauki hankalin jama’ar unguwar ta Kawon Lambu, ta kuma tabbatar da cewa Ruƙayya da Isma’il mutane ne masu jama’a masoya.
A gidan su amarya, an shirya wata ƙwarya-ƙwaryar walima inda mahalarta su ka ci abinci tare da abin sha.
A lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim, ango Afakallahu ya nuna farin cikin sa da Allah ya nuna masa wannan rana ta ɗaurin auren sa da Ruƙayya.
Sannan ya yi godiya ga dukkan jama’ar da su ka halarci ɗaurin auren.

Shi dai wannan aure, ba kowa ba ne ya san za a yi shi saboda yadda ma’auratan su ka ja bakin su su ka yi gum a kan shi, har sai da mujallar Fim ta fara ba da labarin soyayyar Afakallah da Dawayya, daga nan duk duniya ta ɗauka. To ga shi Allah ya kawo wannan rana.
Mu na fatan Allah ya ba su zaman lafiya da kwanciyar hankali.




