YAU dai Allah ya yi, makaɗi kuma mawaƙi Nafi’u Abdulhamid, wanda aka fi sani da suna Bigi, ya angwance.
An ɗaura auren sa da sahibar sa Nana Firdausi Rilwan a yau Asabar, 15 ga Fabrairu, 2020 da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a masallacin unguwar Mahuta da ke kusa da Asibitin Ido (Eye Centre), Kaduna a bisa sadaki N60,000.
Tun a ranar Juma’a, 14 ga wata an yi bikin Ranar Mawaƙa da ‘yan fim a Mogadishu Layout da ke cikin garin Kaduna.
Da ya ke bikin na mawaƙa ne, sun baje kolin su.

An fara bikin da misalin ƙarfe 7:00 na dare, aka cashe har zuwa ƙarfe 9:30 na dare.
Mawaƙan da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Ɗanlaɗiyo Mai Atamfa, Musa Mairabo, Sani DBC, Ɗayyabu Olatunji, Isma’il A.E.C, Ibrahim Ɗanguziri, Auwal Hannun Dama, Auwal Fresh, Yahaya Mai Ganga, Mas’ud, Mai Atamfan Rigachikun da sauran su.
Nafi’u Bigi dai ƙane ne ga ɗaya daga cikin hadiman jarumi Adam A. Zango, wato Murtala Buloko.
Tun a farkon shekarar nan ta 2020 Bigi ya fara sanar wa da abokan sana’ar sa cewa auren sa ya kusa.
Allah ya ba ma’auratan zaman lafiya.

