KA na naka, Allah ya na nasa. A yayin da tauraron mawaƙiya kuma jaruma Hajara Idi Moris ya fara haskawa, sai ga shi aure ya zo bagatatan, za ta yi aure nan da kwana huɗu.
Hajjo za ta cika burin mahaifin ta, wanda ya rasu da ƙawazucin ta yi aure.
Za a ɗaura auren Hajara Idris da angon ta Mika’il Nura a ranar Asaba, 4 ga Satumba, 2022 da ƙarfe 1:00 na rana a gida mai lamba LM 6, Titin Gwarzo, Tudun Wada, Kaduna.
Idan masu karatu ba su manta ba, a ranar Laraba, 24 Agusta, 2022 mujallar Fim ta kawo hira da Hajjo, inda a ciki ta ce, “Ni na fi so in yi aure ne, don mahaifi na ya rasu da burin haka.”
Haka kuma da aka ce mata duk da yake ta na son samu ɗaukaka a masana’antar fim, yaya za ta yi idan miji ya zo, shin za ta bar harkar ne ta yi aure, sai ta ce: “Ai ɗaukakar Allah ta fi ta kowa. Mu duk abin aka ce Allah da Manzon sa, magana ta ƙare. Ai Allah ne ya ce a yi aure, kuma za mu yi aure. Ɗaukakar Allah ya fi komai, in na samu ɗaukaka zan samu kuɗi kuma in yi suna a duniya, in yi suna a duniya in kasa yin suna a lahira, wane ka ga ya fiye min? Suna a lahira shi na ke nema. Idan Allah ya sa na samu miji, kuma ina da shi a hannu na zan zauna da zuciya ɗaya babu tunanin wani abu.”
To, ga shi ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba Allah ya amsa addu’ar ta, mijin ya zo.
Allah ya sa a yi a sa’a, amin.