MINISTAR Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce ma’aikatar ta ba ta amshi gudunmawa ko ta sisi, a nan cikin gida da kuma ƙasashen waje, da sunan tallafin korana ba.
Sadiya ta bayyana haka a lokacin da ta ke kare kasafin ma’aikatar ta na shekarar 2021 a gaban kwamitin Majalisar Tarayya.
Ministar ta yi wannan iƙirari bayan Nijeriya ta karɓi bilyoyin kuɗaɗe a matsayin kuɗaɗen gudunmawar tallafi da yaƙi da cutar korona daga hannun kamfanoni, bankuna da ɗaiɗaikun jama’a.
Sadiya ta ce ko sisi ba a bai wa ma’aikatar ta ba a cikin kuɗaɗen waɗanda wasu ɗaiɗaikun jama’a da kamfanoni su ka bayar gudunmawa.
Ya zuwa ƙarshen watan Afrilu, kuɗaɗen da Nijeriya ta tara daga gudunmawa, sun kai naira bilyan 27.160.
Ta ce amma ba a bai wa ma’aikatar ta ko sisi ba.
Wasu da su ka bada gudunmawa mai tsoka sun haɗa da Aliko Ɗangote, Abdulsamad Rabiu, Segun Agbaje (GTB), Tony Elumelu (UBA), Oba Otudeko (First Bank), Jim Ovia (Zenith Bank), Herbert Wigwe (Access Bank) da kuma Femi Otedola (APD).
Da ta ke magana a kan rabon tallafi, cewa ta yi ma’aikatar ta abinci kawai ta karɓa daga hannun Gwamnatin Tarayya.
“Ba mu karɓi ko sisi ba, amma mun karɓi kayan abinci,” inji ministar.
Ta ƙara da cewa baya ga kasafin ma’aikatar, ba su karɓi ƙarin kuɗi ko naira ɗaya daga hannun Gwamnatin Tarayya da sunan kuɗaɗen tallafin raba wa jama’a ba.
Sadiya ta ƙara da cewa daga cikin kasafin ma’aikatar, kashi 50 kaɗai ta iya karɓa daga hannun Gwamnatin Tarayya.