FITACCEN mawaƙin hip-hop, Ibrahim Rufa’i Balarabe, wanda aka fi sani da sunan Deezell, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewar shi ne ya saki bidiyon nan na tsiraicin Maryam Booth.
A jiya ne soshiyal midiya ta cika da kwakwazo kan ɓullar wani guntun bidiyo na fitacciyar jarumar ta Kannywood inda aka gan ta zigidir a wani ɗaki, ta na ƙoƙarin ƙwace wayar da wani ko wata ke ɗaukar ta.
A yau kuma sai wasu su ka riƙa yaɗa zargin cewar wai fitaccen mawaƙi Deezell ne musabbabin shigar bidiyon a kafafen yaɗa zumunta na zamani.
A jiya mujallar Fim ta bada labarin da babu wanda ya bada irin sa cewar jami’an tsaro na farautar wasu matasa biyu, mace da namiji, waɗanda ake zargin su ne su ka saki bidiyon.
Mujallar ta ruwaito shugaban ƙungiyar jaruman fim reshen Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya na faɗin cewa matasan sun shafe shekaru uku su na karɓar kuɗin toshiyar baki daga hannun Maryam tare da barazanar cewa za su saki bidiyon a gari idan har ta daina ba su kuɗin.
To a yau kuma sai wasu kafofin soshiyal midiya su ka baza labarin cewa wai shi Deezell ɗin ne ya saki bidiyon.
Ɗaya daga cikin kafofin, wato ‘Hausa Loaded’, ta bada labarin cewa wai Deezell ya yi soyayya da Maryam a tsakanin 2016 da 2017, amma su ka ɓata.
Kafar ta ce da su ka ɓata sai ya ɗauki hayar wata yarinya domin ta samo masa hoton Maryam Booth tsirara, abin da yarinyar ta aikata.
Wai da ya samu hoton sai ya dinga neman kuɗi a wajen Maryam tare da bazaranar idan ta hana shi zai ɗau mataki.
Kafar ta ƙara da cewa a shekarar nan da ta gabata ta 2019 Maryam ta yi wa kamfanin Ajino-moto talla, aka biya ta naira miliyan 25.
Wai sai nawaƙin ya buƙaci ta ba shi naira miliyan 10 daga ciki, ita kuma ta faɗa masa ba ta da irin wannan kuɗin.
Wai a dalilin haka ne ya fara tura wa abokan sa bidiyon.
To amma dai Deezell ya ce wannan labari duk zuƙi-ta-malle ce.
A wata sanarwa da ya bayar a Twitter da Instagram, Deezell ya ce, “An jawo hankali na ga wani bidiyon tsiraici na jarumar Hausa Maryam Booth wanda ke yawo a kafofin soshiyal midiya tare da ƙazafin cewa wai ni ne na saki bidiyon.
“Sai dai kuma abin baƙin ciki shi ne su waɗannan masu mugun nufin, waɗanda wakilan jawo bala’i ne, sun kasa kawo duk wata shaida ko hujjojin cewa ni ɗin ne wanda ya saki bidiyon da ke yawon.
“Da yake kyakkyawar manufa na buƙatar amsa, ina so in bayyana ƙarara cewa ba ni ba ne wanda ya saki bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, kuma a gaskiya a iya sani na ban san wanda ya sake shi ɗin ba.
“A matsayi na na Musulmi, na sani cewa ya saɓa wa Alƙur’ani Mai Tsarki da koyarwar Annabin mu Muhammadu (tsira da aminci su tabbata a gare shi) mutum ya yaɗa ko ya saki abin da bai dace ba na wani mutum a bainar jama’a, musamman a soshiyal midiya, da nufin musguna masa.
“Haka kuma wannan mugun zargin da ake mani na yaɗa tsiraicin ‘yar’uwa ta Musulma gaba ɗaya ƙarya ne ta kowace fuska, kuma ina so kowa ya sani cewa waɗannan zarge-zargen duk ƙarya ne.
“Duk da yake ban san dalilin da ya sa ake mani wannan zargi ba, ina kira ga waɗanda ke yaɗa wannan ƙazafin da su janye maganar su, kuma su ba ni haƙuri cikin awa 12 ta hanyar soshiyal midiya ba tare da ɓata lokaci ba.
“Idan su ka ƙi kuwa, babu abin da zai rage mani illa in ɗauki matakin shari’a da su don in kare mutunci na da na sha wahala na samu.
“A ƙarshe, ina tausaya wa wadda wannan ibtila’i ya faɗa wa tare da yin kira a gare ta da ta binciki wanda ya saki bidiyon da ke yawo, kuma ta ɗauki matakin dukkan shari’a da ya dace a kan waɗanda su ka aikata mata hakan.”