JARUMAR Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta nesanta kan ta da wani jerin sunaye da jaridar ‘Punch’ ta buga mai nuna cewa ta na ɗaya daga cikin mata ‘yan fim da ɗan takarar zama shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa a matsayin matan da za su taya shi kamfen.
Rahama ta ƙaryata labarin ne a soshiyal midiya, a wani saƙo da ta yi da Turanci inda ta ce: “This is a fat big lieeeee…. I am not aware of this… I don’t know how my name made it to this list. Not in any way associated with this.” Ma’ana: “Wannan babbar ƙarya ce. Ni ba ni da masaniyar wannan. Ban san yadda aka yi suna na ya shiga wannan jerin ba. Babu abin da ya haɗa ni da wannan abin.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ba a san jarumar da shiga harkar siyasa ba, sannan da alama ba a tuntuɓe ta ba kafin a fitar da sunayen, wanda hakan ne ya sa ta yi wannan rubutu cikin ɓacin rai da mamaki.
Ban da ita Rahama, wasu mata ‘yan Kannywood da ke cikin jerin sun haɗa da Saratu Giɗaɗo (Daso), Kyauta Dillaliya, Samira Ahmad, Fati Nijar, Mansurah Isah, Teema Makamashi, Ummi Gombe, Hadiza Kabara, Fati Karishma, Samira Saje, da Hajiyan Nas.

Sai dai kuma tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta yi wa Rahama, ta ce mata kuskure ne da aka saka sunan Rahama a jerin.
A cewar Mansurah: “Zuwa ga Rahama, da ma ba sunan ki ba ne wanda ki ka gani. Sunan Rahama MK ne amma da yake ke kaɗai ce Rahamar da su ka sani a Kannywood, sai su ka ɗauka ke ce. Amma kada ki damu, ba ke ba ce.”
Mansurah, wadda ta yi dumu-dumu a harkar siyasar Tinubu, ta nuna cewa su ne su ka ba da sunayen da aka gani, kuma ba su ba da sunan Rahama Sadau ba saboda sun san ita ba ta harkar siyasa.
A cewar ta, ‘yan Kudu ne su ka buga sunayen, shi ya sa su ka yi kuskure, domin ba su san Rahama MK ta cikin diramar ‘Kwana Casa’in’ ba.
Rahama Sadau dai ba ta ce wa Mansurah komai ba.
Amma ita Rahama MK, sai murna ta ke yi, domin har ta kwafe sunayen ta wallafa a shafin ta tare da godiya.
Idan kun tuna, a makon jiya mun ba ku labarin yadda aka naɗa ‘yan Kannywood biyar a matsayin waɗanda za su shiga rundunar yaƙin neman zaɓen Tinubu a babban zaɓen shekara ta 2023.
Su ne: Dauda Adamu Abdullahi (Rarara), Jadda Garko, Sani Idris Kauru (Moɗa), Nuhu Abdullahi, da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Isma’ila Na-Abba (Afakallahu).
Comments 2