• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Babban buri na in ga ranar aure na – Malam Tsalha na ‘Daɗin Kowa’

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 30, 2021
in Taurari
1
Ahmad Isma'ila Baso (Malam Tsalha)

Ahmad Isma'ila Baso (Malam Tsalha)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MALAM Ahmad Isma’ila Baso ya yi fice a matsayin ɗaya daga cikin jaruman fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Daɗin Kowa’ na gidan talbijin na Arewa24. Ɗan wasan, wanda aka fi sani da Ɗanlele a Kannywood kuma Malam Tsalha a ‘Daɗin Kowa’, ya na cikin ‘yan sahun gaba na waɗanda su ka bada gudunmawa wajen kafuwar masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. 

Ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Albasu da ke Jihar Kano, an haife shi a cikin 1972 kuma ya yi karatun boko da na Islamiyya a Kano. Daga nan ne ya fara gwagwarmayar rayuwa har ta kai ga ya tsinci kan sa a harkar fim.

Jarumin ya ɗauki tsawon shekaru ana harkar fim da shi ba tare da masu kallo sun san fuskar sa ba har zuwa lokacin da ya fara fitowa a cikin ‘Daɗin Kowa’ a matsayin bafaden maigari.

Mujallar Fim ta tattauna da Malam Ahmad a kan faɗi-tashin da ya yi kafin zuwan sa wannan matsayi, da irin abubuwan da su ke ci masa tuwo a ƙwarya a rayuwar sa, kamar haka:

FIM: Mai karatu zai so jin labarin yadda aka yi ka tsinci kan ka a cikin Kannywood.

MALAM AHMAD: Bayan na gama karatu na na sakandire, na samu aiki a wani kamfanin haɗa atamfa a unguwar Sharaɗa Phase 3. Daga baya kuma aka rufe kamfanin, na dawo gida da zama.

To, da man kuma can ni ma’abocin kallon rawar ƙoroso da dirama ne. Tun ana yi a gidan maza na ke zuwa kallo har ta kai ga abin ya ba ni sha’awa na shiga, mu na fafatawa. Daga nan kuma mu ka tashi mu ka koma unguwar Tukuntawa. Nan ma mu ka tashi mu ka koma Gidan Zu. Shi ma mu ka tashi mu ka koma Filin Hoki. Ba na mantawa, a lokacin marigayi Rabilu Musa Ibro, nan ya ke zuwa a kan keken sa da kayan sa ya na roƙon mu da mu sa shi, ana korar sa har ta kai ga wata rana ogan mu ya sa shi sau ɗaya. Sai aka ga ashe ya na da abin dariya, kuma shi burin sa a lokacin shi ne ya ga an sa shi ba tare da an ba shi kuɗi ba.

To daga nan ne kuma mu ka tashi mu ka koma gidan wasan da ke Lahai.

Bayan da mu ka koma Lahai mu na ƙoroso da dirama, lokaci guda sai marigayi Tijjani Ibraheem su ka zo da shi da oga Kunle da wata Doba rediyon sa, su ka sa kaset su ka ce za a yi rihazal. Mu ka ce, “Darakta, menene kuma rihazal?” Ya ce, “Waƙa ce za a sa a kaset ana bin ta tare da yin rawa.”

Nan fa aka fara yi. Ana yi har sai da ta kai ya ture mana ƙoroson mu gefe. Har ta kai ga tafiya ta yi tafiya mun zama ogannin kan mu, mu na bayar da yara idan jarumi zai yi fim kamar su Ali Nuhu, Sani Danja, Adam A. Zango da sauran su, su zo idan za su yi fim su kawo mana kaset na zare mu yi kwana uku mu na koya wa yara irin rawar da ta dace da wannan waƙar. Sai kuma mu ba su yaran mu. To ka ji yadda aka yi na tsinci kai na a wannan masa’anta.  

FIM: A wancan lokacin a iya rawa ka tsaya ko har da yin fim?

MALAM AHMAD: A lokacin ni ai na shige matakin yin rawa, sai dai na koyar. Wanda ba na mantawa shi ne wanda na fara ba wa Adam A. Zango yaran da su ka yi masa rawa a fim ɗin sa na farko, ina jin sunan fim ɗin ‘Surfani’, wanda kuma daga baya gidan Lahai ya rushe, wato inda mu ke wannan rawar kenan da dirama.

Sai kuma na yi tunanin cewa ni fa da man fim na ke so na yi. Kawai sai wata dabara ta zo mani. Na yi wanka na sa kayan sut. A lokacin a Kannywood gaba ɗaya ba wanda bai san ni ba a Ɗanlele. Idan na sa kwat ɗi na a jiki na, sai na fita domin jin inda ake lokeshin. Kamar na ji yau Yakubu Muhammad ya na lokeshin, sai na hau ɗan acaɓa na tafi. In na je ya ɗan gan ni tsaf-tsaf da ni sai ya ce, “Ɗanlele zo ka min sin ɗaya.” To a haka mu na yi mu na yi har ta kai ana ɗan kira na.

Mu ka haɗe da Alhaji Garba Ɗansanda mu ke yin fim. Wani lokacin ma idan na je wani garin na ga mutane ba su gane ni ba, sai na ce musu ni ne wane fa wanda ya fito a likita a fim kaza, ko ɗan sanda. Sai ka ji ana, “Haka ne fa!” To ka ji yadda aka yi na fara harkar fim.

FIM: An ɗauki tsawon lokaci ba a ga Ɗanlele a cikin fim ba, wanda da har ana cewa ko ka daina fim, sai kuma kwatsam aka ga ka dawo cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa24 a matsayin Malam Tsalha. Ya aka yi aka haihu a ragaya?

MALAM AHMAD: Yadda na tsinci kai na a cikin fim ɗin ‘Daɗin Kowa’ na Arewa24 shi ne a lokacin tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau, kowa ya sani a lokacin an hana mu yin fim a Kano in ban da su Ibrahim Maishunku da wasu tsiraru da ake kai su kamar Kaduna ko Jos da Abuja su je a yi fim. A lokacin nan sai Kannywood ta wargaje. Sai na ga harkar duk ta ma fita daga rai na. Na tafi hutu. 
To bayan na dawo kuma, lokacin gwamnatin Kwankwaso, akwai wani yaro ana ce da shi Haidar, su na wani lokeshin da AGM Bashir, sai ya min waya ya ce don Allah na zo zan fito a boka. Na zo na yi. Bayan mun dawo da magariba Gidan Ɗan’asabe, da man a nan mu ke haɗuwa, sai na haɗu da wani aboki na mai suna Adam M. Adam, wanda ake kira ‘Trooper’, wanda shi ne daraktan ‘Daɗin Kowa’. Sai ya ce, “Ɗanlele, ina ka shige ne?” Sai na ce, “Aboki na, wallahi harkar ce kawai ta fita daga rai na.” Sai ya ce, “Haba, ka zo mana. Akwai gidan talbijin na Arewa24 mu na nan mu na aiki. Na ce masa to. Mu ka yi musayar lambar waya.

Kwatsam, ya kira ni ya ba ni sikirif na duba. Na ga zan fito a farkon bazawarin Hafsatu matar tsohon soja. Da wannan na fara.

Ahmad malamin rawar ƙoroso ne kafin ya shiga harkar fim

FIM: Shin akwai wani fim da ya fito da kai mutane su ka san ka tun bayan fara fitowar ka a fim?

MALAM AHMAD: Babu. Wannan fim na ‘Daɗin Kowa’ shi ne ya fito da ni har ta kai mutane su ka san ni, sanadiyyar canza min rol da aka yi a cikin shirin, wanda shi mai bada umarni, Adam A. Adam, ya canza mani daga wancan bazawari zuwa Malam Tsalha, aka kuma maida ni fadar maigari. 

Sai dai kuma a baya darakta Salisu T. Balarabe ya yi mani magana cewa ya ajiye min wani rol wanda da ni zan fito a matsayin Kofur Audu saboda ya san da na iya aktin na ɗan sanda. To kuma can shi Trooper, ya riga ya ba ni wannan matsayin na Malam Tsalha, har ta kai ga Salisu T. Balarabe ya yi fushi ya ce, “To a ga wanda zai kira ka”, tunda shi Salisu ya na da ƙarfin faɗa a ji a tashar, shi kuma Trooper bai da wannan kamar Salisu.

To, da na ga haka kawai sai na koma na duƙufa zuwa ga Allah, na yi ta addu’a ina cewa Allah ya sa na samu wannan fim ɗin ya kuma zama silar da mutane za su san fuska ta a duniya. Sai gashi haƙo na ya cimma ruwa tun bayan da aka kira ni na fara wannan fim ɗin. Wannan fim ɗin na ‘Daɗin Kowa’ shi ne silar ɗaukaka ta.

FIM: Ya mutane su ke kallon ka a gaske a matsayin da ka ke takawa na Malam Tsalha, munafuki mai haɗa mutane da ‘yan’uwan su idan kun haɗu?

MALAM AHMAD: Gaskiya mutane da yawa su na yi mani wani kallo wanda ba sa fahimta ta sosai. Kuma ni babban baƙin ciki na ma shi ne yara idan mu ka haɗu da su su na rububi na, ana ta hotuna ana waye; sai mun rabu nan da can in na tafi na bar su sai ka ji sun ce, “Munafukin ‘Daɗin Kowa!” Sai na ji kamar an caka min wuƙa a ƙirji na. Ba na son irin wannan domin ni a rayuwa ta ma wallahi na tsani munafurci kwata-kwata a rayuwa ta.

Lokuta da dama idan an faɗa min wani munafurcin ma da zan yi lokacin da za a ɗauki fim ɗin sai na je na ce wannan abin fa ya yi yawa, ba za a rage ba?” Sai su ce na yi haƙuri saboda saƙon nan in ba ta hanyar ka ba ba ta yadda za a yi ya fita.

‘Yan’uwa na da yawa da abokanai na idan sun haɗu da mutane su na gaya min cewa wai anya a gaske ni ba munafuki ba ne? Sai su dinga kare ni. Kuma har ga Allah ina jin daɗin abin da su ke yi min na kare ni a gun jama’a.

FIM: Ka na jin daɗin wannan matsayi da ka ke takawa na munafuki kuwa?

MALAM AHMAD: To farko dai ka ga ni a matsayin ɗan fadar maigari na fito. Akwai wani mai suna Saugiji wanda shi ne mahaifin Sahabi a ‘Kwana Casa’in’ wanda rol ɗin sa irin dattijo ne a layi wanda ya ke sa ido. Sai aka cire shi. Akwai kuma Ɗan Bayero, wato ɗan kai rahoto. To sai su kuma marubuta su ka ga Ɗan Bayero bai dace da wannan rol ɗin ba, ba ya musu abin da su ke so kawai aka haɗa min rol biyu: ni ne ɗan fada, ni ne kuma ɗan gani ba ƙyalewa, ɗan kai rahoto ta bakin Kyauta kuma guntsi fesar (dariya).

Gaskiya duk wanda ya fahimce ni, ina jin daɗin abin da na ke yi tunda fim na ke yi.

Ina haɗuwa da mutane kala-kala, su na gani ina fashewa da dariya ake yi da yanayin rol ɗi na. 

To, alhamdu lillahi, duk wanda na gani sun yi dariya na san cewa sun san fim ne, a gaske ba haka na ke ba. Kuma jarumi idan ya san ya fito ko akwarto ko a munafuki ko ɓarawo, to fa kar ya sake ya yi abin nan ko da da wasa, saboda mutane za su yi masa kallon irin abin da ya ke yi a fim a gaske ma halin sa ne. Don haka ni ina kaffa-kaffa da abin da za a ce ni na ce kaza.

FIM: Bayan fim ɗin ‘Daɗin Kowa’ a cikin wannan masana’anta, ana kiran ka ka yi fim?

MALAM AHMAD: E, ana kira na sosai, kama daga finafinan barkwanci da na ‘yan YouTube da sauran su saboda ita tashar Arewa24 ta ba mu dama na je na yi fim na fito a duk wani abu da aka ban na taka rawa a kan sa, sai dai ban da suna na na Malam Tsalha. Amma in ma munafuki ka ke so na fito a cikin fim ɗin ka, kawai suna za ka canza min, ni kuma in Allah ya yarda zan yi.

FIM: Shin ko an samu nasarori daga fara wannan fim? 

MALAM AHMAD:  Na samu. Da man babban burin ɗan fim shi ne ya ga duk inda ya shiga ya ji jama’a su na ga wane. To wannan shi ne babbar nasara. Sannan kuma a ce ka na da rai da lafiya kuma rol ɗin ka ka na ci gaba da takawa ka na ba wa ɗan kallo nishaɗi kuma ka na ba wa marubuci abin da ya ke so ka yi, shi ma darakta ka na ba shi abin da ya umarce ka ka yi. Wannan ma kan sa riba ce a gare ka. 

Kuma da man yanzu fuskar ta fashe, sai a hankali, amma mu na samun masoya na ɗaukar hoto mu ke haɗuwa da su, ba wai waɗanda ake samun abubuwa a gun su ba; su ma mu na fatan nan gaba za mu samu.

FIM: A ɓangaren ƙalubale kuma fa?

MALAM AHMAD: To wasu su na ce mani in daina zuwa ko ina aka kira ni ina fitowa a matsayin munafuki: “Ai bai kamata a ce an ba ka matsayi ɗaya ba”. Sai na ce ai su a irin wannan kastin ɗin su ka gan ni kuma su ke sha’awar na yi musu. Kuma ai na samu izini daga ita tashar da aka san ni da haka.

FIM: Wane buri ka ke da shi a rayuwa? 

MALAM AHMAD: Yanzu ni ba ni da aure, kuma ba ni da wani buri a yanzu da ya wuce a ce yau na yi aure.

FIM: Ka taɓa yin auren ne ko ba ka taɓa yi ba?

MALAM AHMAD: Gaskiya ban taɓa yin aure ba, haka kuma Allah ya tsaga, domin kuwa da akwai wata da ta taɓa zama a gidan ƙanwa ta kuma yanayin ƙanwa ta yadda mu ka shaƙu da ita ta ga cewar ya kamata na auri wannan yarinyar. Yarinyar ta na so na, ina son ta. To ashe baban ta ya riga ya yi mata miji, mu ba mu sani ba, kuma uwar ta ta fi so na auri ‘yar tata kamar yadda ta ga cewa ta yaba da hankali na. Mu ka je mu ka sayo irin kayan ka-gani-ina-so ɗin nan, abubuwa dai sosai. Kuma daga ƙarshe ban aure ta ba. Yanzu haka ma ta na da ‘ya’ya biyu.

FIM: Yanzu ka samu wacce ka ke so ka aura?

MALAM AHMAD: Akwai dai mata aƙalla 15 da su ke so na, amma ni har yanzu ban tantance ba saboda yanzu da wahala ka samu wacce ta ke son ka tsakani da Allah. Amma dai akwai mata guda biyu da na ji ina so. Ina dai addu’ar Allah ya zaɓan mafi alkairi.

FIM: A ƙarshe, wane saƙo ka ke da shi ga jama’a?

MALAM AHMAD: Saƙo na shi ne su yi haƙuri a kan abin da aka ba ni, su yi haƙuri, ba haka na ke a waje ba, su yi min kyakkyawar fahimta.

A ɓangaren ‘yan fim kuma, don Allah don Annabi su san me su ke yi. Duk abin da za su yi, su ɗauka sana’a su ke yi. Kamar kai ne a ɗauke ka a kai ka gona ka yi aiki, tsakani da Allah ko shago ka kare wa mutane kayan su da mutuncin kan ka. Na gode.

Loading

Tags: Ahmad Isma'ila BasoArewa24 TVaureDadin Kowa moviehausa filmsKannywoodMalam Tsalha Dadin KowaRabilu Musa IbroSalisu T. Balarabe
Previous Post

Hidimar da Charles Henry Robinson ya yi wa harshen Hausa

Next Post

Ranar ‘yancin ƙasa da kuma wasu ‘yan tsirarun mutane da ke cikin ta

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Shugaba Muhammadu Buhari tare da iyalan sa sun yi shigar fari da tsanwa, su ka ɗau hoto don murnar cikar Nijeriya shekaru 61 da samun mulkin kai... a Fadar Shugaban Ƙasa a yau

Ranar 'yancin ƙasa da kuma wasu 'yan tsirarun mutane da ke cikin ta

Comments 1

  1. Dan Lanjeriya says:
    4 years ago

    Tirkashi: Kai kuwa Malam Tsalha yanzu fisabilillahhi ace har yanzu kai gwauro ne ko tuzuru? Kai ba yadda kaso ba…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!