FATI Bappa Fagge ta bayyana cewa labarin da aka yaɗa a yau cewar wai ta rasu ba gaskiya ba ne, kawai ji-ta-ji-ta ce maras tushe.
A safiyar wannan rana ta Litinin, 15 ga Yuni, 2020 aka wayi gari da wani labari da ya ke yawo a soshiyal midiya, inda aka yaɗa cewar wau fitacciyar jarumar, wadda aka fi sani da Fati Bararoji, ta rasu.
Labarin dai a lokaci guda ya yi ta yaɗuwa kamar wutar daji, wanda hakan ya sa masoya da ‘yan’uwan tsohuwar jarumar su ka samu kan su a cikin wani yanayi.

To sai dai da mujallar Fim ta tuntuɓi jarumar ta wayar ta ta tabbatar mana da cewa labarin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne.
A cewar ta, ita ta na nan a gidan ta cikin ƙoshin lafiya.
Bugu da ƙari, Fati ta saki wani guntun bidiyo a cikin wannan rana inda ta yi godiya ga Allah bisa halin da ta samu kan ta, sannan ta yi godiya ga ɗimbin masoyan ta da su ka nuna mata ƙauna dangane da mugun labarin da su ka samu game da ita har su ka yi ta kiran ta don su ji halin da ta ke ciki.
Daga ƙarshe, ta musanta labarin da ake yaɗawa.