FITACCEN mawaƙi a Kannywood, Hussainin Danko, ya ce shi Allah ne ya yi masa baiwar waƙa, don haka ba sai ya tsaya rubutawa ba.
Mawaƙin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mijallar Fim, inda ya ce: “Ni Allah ne ya yi mini baiwar waƙa, don haka duk lokacin da na zo yin ta kawai zuwa ta ke yi ba tare da na shirya ba.
“Don haka ba na tsayawa rubutun waƙa, domin wani lokacin ma har mantawa na ke yi ni mawaƙi ne sai na zo na zauna a situdiyo, sai ka ga Allah ya kawo baiwar na yi ta kai-tsaye. Don haka ba na rubuta waƙa.”

A ɓangaren abokan sana’ar sa mawaƙa kuwa, Hussaini ya yi kira a gare su da su kyautata waƙoƙin su wajen kare mutuncin sana’ar saboda mutane su riƙa ganin ƙimar su.
Haka kuma ya ja hankalin masoyan mawaƙan Kannywood da su riƙa yi masu gyara, ba wai kullum su riƙa yabo ba.
Fasihin mawaƙin ya yi fatan Allah ya haɗa kan abokan sana’ar sa mawaƙa domin a samu cigaba a cikin harkar tasu.