NA je na kai masa ziyarar duba shi a asibiti awa ɗaya kafin mutuwar sa.
Ko da na shiga asibitin na tarar da iyayen sa, matan sa, ‘yan’uwa, aminai da abokan mu’amula wasu su na kuka, wasu cikin damuwa, wasu kuma su na ta ba shi kalmar shahada.
Amma duk da yanayi na sharafa da ya ke ciki, Allah bai sa ya ɗimauce ko fita cikin hankali ba. Ya yi maganganu na bankwana, wasiyya, bushara da neman afuwar waɗanda ya saɓa wa tare da yafe wa waɗanda su ka ɓata masa.
Ya faɗi cewa zai mutu ba sau ɗaya ba. Babban abin da ya ba ni mamaki shi ne ba ya na faɗin zai mutu saboda zafin ciwo ba, duk lokacin da zai faɗi kalmar zai mutu ya na faɗin kalmar cikin farin ciki da fara’a!
Duk da tsananin ciwo da halin da ya ke ciki a lokacin sallar la’asar ya yi sallah. Bayan ya idar da sallah, ya ce, “A ci gaba da salati da hailala da ake yi.”
Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!A cikin wannan yanayin Allah ya karɓi ran Isiyaku Forest. Ya mutu ya na kalmar shahada cikin farin ciki, fuskar sa cike da haske da annuri.
Ban yi mamakin kyakkyawan ƙarshe da cikawa da imanin da ya yi ba, duba da irin babbar shaida da ya samu a wajen mahaifiyar sa na matuƙar biyayya da kulawa da ɗawainiya da ya yi da ita da ‘yan’uwan sa da sauran abokan arziki.
Ya Allah, ka jiƙan Isiyaku Forest. Ya Allah, ka sa mutuwa ta zamo hutu gare shi. Ya Allah, ka sa mu ma mu yi kyakkyawan ƙarshe, mu cika da imani da kalmar shahada, saboda alfarmar Manzon Allah (s.a.w.).
* Malam Sadiq Zazzaɓi fitaccen sha’iri ne da ke zaune a Kano
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazin.com
Amin amin. Allah saka masa da aljanna mafi girma