• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Banka wa ofis ɗin mu wuta a Inugu koma-baya ne, inji INEC

by DAGA WAKILIN MU
May 14, 2021
in Nijeriya
0
Banka wa ofis ɗin mu wuta a Inugu koma-baya ne, inji INEC
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana gobarar da aka yi a ofishin ta na Ƙaramar Hukumar Udenu da ke Jihar Inugu a matsayin wani sabon koma-baya a tsare-tsaren da ta ke yi na shirya zaɓuɓɓukan da ke tafe nan gaba.

Hukumar ta faɗi haka ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, Babban Kwamishinan ta mai kula da Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe, ya raba a ranar Juma’a.

Okoye ya bayyana damuwa kan yadda yawan ƙona kayan hukumar a wasu jihohi ta hanyar gobara ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Ya ce, “Yanzu kuma a Jihar Inugu abin ya faru, inda Zaunannen Kwamishinan Zaɓe na jihar, Mista Emeka Ononamadu, ya kawo rahoton cewa an banka wa ofishin INEC na Ƙaramar Hukumar Udenu wuta.”

Ya ce abin baƙin cikin da ya faru ɗin ya auku ne wajen kimanin ƙarfe 8:40 na dare a ranar Alhamis, amma ba a samu salwantar rai ba.

Amma, a cewar Okoye, an yi matuƙar lalata ginin ofishin, kuma kayan zaɓe da na aikin ofis duk sun ƙone duk da ƙoƙarin da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Inugu ta yi wajen kashe gobarar.

Ya ce INEC ta ji daɗin ƙoƙarin da hukumar ‘yan kwana-kwanan ta yi.

Okoye ya ce an sanar da ‘yan sanda abin da ya faru domin su yi bincike.

Ya ce, “Wannan shi ne karo na uku da  ake sanya wa ofisoshin INEC wuta a ƙananan hukumomi da ke jihohi uku a cikin ƙasa da mako biyu.

“Na farko, an lalata ofis ɗin mu na Ƙaramar Hukumar Essien Udim da ke Jihar Akwa Ibom a ranar 2 ga watan Mayu.

“Daga nan sai wutar da ta tashi a ofishin mu da ke Ƙaramar Hukumar Ohafia na Jihar Abiya a ranar 9 ga Mayu.

“Wannan wani ƙarin koma-baya ne ga ayyukan da hukumar ke yi da shirye-shiryen ta na zaɓuɓɓukan da ke tafe.”

Okoye ya tuno da cewa bayan harin da aka kai a Abiya, hukumar ta yanke shawarar ta kira wani taron gaggawa na kwamitin tuntuɓar hukumomin tsaro kan zaɓe, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES) a makon gobe domin tattauna wannan abin damuwar wanda ke faruwa.

Ya ce lalata gini da kayan aikin hukumar da ya faru a yanzu a Jihar Inugu ya na buƙatar a yi saurin duba matakan da su ka kamata don tsare kayan INEC a dukkan jihohin ƙasar nan.

“Saboda haka, hukumar za ta kira taron gaggawa na dukkan zaunannun kwamishinonin ta, wato ‘Resident Electoral Commissioners’ (RECs) a ranar Laraba, 19 ga Mayu, a Abuja kafin taron kwamitin na ICCES.”

Sai dai babban kwamishinan ya bayyana ƙudirin hukumar na ci gaba da aiwatar da ayyukan da aka ɗora mata, cikin su har da kammala aikin ƙara yawan rumfunan zaɓe.

Sauran, a cewar sa, sun haɗa da ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR), da ayyukan ƙara wa ma’aikata ƙarfin aiki, da sake duban fasalin Babban Tsarin Aiki (Strategic Plan) na 2022-2026, da ƙarfafa hulɗa da masu ruwa da tsaki da kuma gudanar da dukkan zaɓuɓɓukan da aka tsara za a yi.

A wani labarin mai alaƙa da wannan, an ruwaito Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Inugu, Mista Mohammed Aliyu, ya bada umarnin a binciki gobarar da aka yi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor.

Aliyu ya kuma ce a killace wurin don a samu damar gudanar da bincike don tabbatar da hakikanin abin da ya auku tare da gano irin asarar da aka yi.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, ASP Daniel Ndukwe, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ndukwe ya ce gobarar, wadda ta faru a ofishin INECA da ke Obollo-Afor da ke cikin Yankin Ƙaramar Hukumar Udenu na Jihar Inugu, ta faru ne a ranar 13 ga Mayu, da misalin ƙarfe 9:40 na dare.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda ta samu kiran koke daga babban ofishin ta na yanki da ke Udenu cewa akwai gobara da ta tashi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor a Ƙaramar Hukumar Udenu.

“Nan take jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin yankin su ka garzaya zuwa wajen, yayin da su ka kira Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Inugu su ka je wurin su ka kashe wutar ba tare da ɓata lokaci ba.”

Ya ce an kashe wutar kafin ta yaɗu zuwa sauran ofisoshi da ke kusa da ginin, ta hanyar haɗin gwiwar hukumar ‘yan kwana-kwanan da ‘yan sanda da kuma jama’a da su ka taimaka.

Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewar wutar ta faru ne ta hanyar ƙarfin wutar lantarki da aka antayo zuwa ginin kafin gobarar ta faru.’’

Loading

Previous Post

Eid el-Fitr: Jarumar Nollywood Tonto Dikeh za ta ciyar da ‘ya’yan Musulmi 2,000

Next Post

Asase: Yadda saka finafinai a YouTube ya ceci Kannywood

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Asase: Yadda saka finafinai a YouTube ya ceci Kannywood

Asase: Yadda saka finafinai a YouTube ya ceci Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!